Ƴan Najeriya daga ko ina a faɗin ƙasar sun yi tir yi kan yadda ɗan majalisan dake wakiltar ƙananan hukumomin Dikwa/Kunduga/Mafa a majalisar tarayya ya maida mutanen sa da ya kamata ya daraja kamar kaji da ake watsa wa dawa.
Ɗan majalisa Ibrahim Abunna ya tara jama’ar mazabar sa ɗaruruwan su shi kuma yana saman bena sai ya rika kwance ɗaurin bandir din kuɗi yana watso musu daha sama su kuma a kasa suna ta damben kwasa, mai rabo ka ɗauka.
” A wasu lokutta kamar yadda yake a wannan bidiyo da aka saka a shafukan yanar gizo, an ga sai Honarabul Ibrahim yana kecewa da dariya a duk lokacon da ya hango mutane na damben cafke kudin daga ya watso daga sama.
Masu Karatu da dama sun yi tir da wannan salon raba kuɗi da wannan ɗan majalisa ya yi suna masu cewa da wasu ababaen more rayuwa yayi wa mutanen ko kuma tallafin da zai amfanar da su yayi da ya fi abin da yayi.
” Tsakani da Allah ace wai wakilin jama’a ne ya ke yin haka, ya kalli jama’ar sa Talakawa ya rika watsa musu ₦200 suna warwason shu, shikuma yana kece wa da dariya. Wannan abu bai yi min daɗi ba.
” Wasu masu karatun sun ce da ƴaƴan su ya biya wa kudaɗen karatu, ko kuma ya damka wa iyayen su kuɗaɗe masu kauri su yi sana’a da ya fi irin wannan wulaƙanci da yayi musu, ” Don ni a wuri na wulaƙanci ne da rainin wayau.