Yadda gobara ta tashi a Cocin T.B Joshua, lokacin da ake jana’izar sa

0

Gobara ta tashi a Babban Cocin Synagogue na marigayi T.B Joshua a Legas, daidai lokacin da ake tsakiyar bikin jana’izar sa.

Wutar wadda ta tashi wajen ƙarfe 11 na dare, majiya tace ta tashi ne daga wani ɗakin ajiyar kayayyaki, wanda ke kusa da danƙareren babban ɗakin bautar da ke cike danƙam da jama’a a lokacin.

Ba a dai san musabbabin tashin wutar ba, amma wani da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce wayoyin lantarki ne su ka haɗu, sai tartsatsin wuta ya tashi.

Wutar wadda ta tashi a ranar Litinin dai an samu kashe ta bayan da dandazon masu Bauta a cocin su ka riƙa bazama su na ɗebo ruwa kusa da cocin har su ka kashe wutar.

Sai dai kuma Jami’an Hukumar Kashe Gobara sun isa wurin bayan an kashe wutar, can wajen ƙarfe 12:15 na dare.

T.B Joshua ya mutu ranar 5 Ga Yuni, 2021, kwanaki ƙiris kafin zagayowar ranar haihuwar sa da cikar sa shekaru 58 a duniya.

Share.

game da Author