KORONA TA DAWO GADAN-GADAN: Mutum 772 sun kamu, mutum 2 sun rasu cikin Kwanaki uku a Najeriya

0

Jami’an kiwon lafiya a Najeriya na fargaban sake barkewar cutar korona zango na uku a kasar nan.

jami’an lafiyan sun fara fargaban ne tun bayan da aka samu tabbacin bullowar zazzafar nau’in cutar ‘Delta’ a kasar nan.

Tun bayan haka ne aka fara samu karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da yawan da cutar ke kashewa a kasar nan.

Hukumar NCDC ta bayyana cewa daga ranan Alhamis zuwa Asabar mutum 773 sun kamu sannan mutum 2 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar a kasar nan.

A ranan Alhamis mutum 184 ne suka kamu da cutar daga jihohi bakwai a kasar nan.

Alkaluman sun nuna cewa jihar Legas-124,Rivers -27, Sokoto-9, Abuja -8, Oyo -6, Ekiti-5, Delta-4 da Fitato -1.

A ranar Juma’a mutum 317 ne suka kamu mutum daya ya mutu a jihohi 10 a kasar nan.

Wannan shine karo na farko da Najeriya ta samu yawan mutane irin haka bayan watanni hudu.

Bisa ga alkaluman mutum 172 sun kamu a jihar Legas, Akwa-ibom-62, Oyo-33, Rivers-32, Ekiti-5, Abuja-5, Ogun -3, Sokoto-2, Bayelsa-1, Gombe-1, da Kano-1.

A ranan Asabar mutum 272 sun kamu mutum daya ya mutu daga a jihohi 9 a Najeriya.

Jihar Legas-183, Rivers 62, Oyo-10, Ondo -32, Abia-7, Ogun-7, Ekiti-5, Delta-2 da Filato -1.

Zuwa yanzu mutum 170,895 ne suka kamu, mutum 2,132.

Mutum 164,788 sun warke sannan 3,955 na killace a asibiti.

Hukumar kula da Ingancin Abinci Da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta yi karin haske kan dalilin da ya sa har yanzu bata amince da maganin gargajiya da aka hada domin warkar da cutar korona a kasar nan ba.

Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ya ce har yanzu babu wani maganin warkar da cutar da aka hada a duniya.

Ta ce magungunan da ake da su yanzu magunguna ne da aka hada domin rage raɗaɗin cutar a jiki ba wai ya warkar da ita
Daga nan kuma sai Mojisola ta gargaɗi mutane da su rage yawan amfani da tafarnuwa da albasa wai don warkar da Korona ko yin rigakafin ta.

Daga an ta ce duk wani maganin gargajiya da aka hada domin warkar da korona ba tare da hukumar NAFDAC ta tabbatar da ingancin sa ba ba magani bane.

Sannan yin amfani da maganin gargajiyan da aka hada domin warkar da korona ba tare da an nemi izinin hukumar ba ya karya dokar da hukumar ta saka na kula da ingancin magunguna da abinci a kasar nan.

Mojisola ta yi kira ga mutane da su guji yin amfani da maganin da aka hada ba tare da hukumar NAFDAC ta tabbatar da ingancin sa ba.

Share.

game da Author