Daga ranar Alhamis zuwa Juma’a mutum 1,148 sun kamu mutum 10 sun mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar Korona.
Ga dukan alamu cutar ta sake barkewa a kasar nan zango na uku ganin yadda cutar ta ci gaba da yaduwa a kasar nan.
A dalilin haka ya sa kwamitin dakile yaduwar cutar take fargaban cewa gwamnati za ta iya sake saka dokar zaman gida dole domin dakile yaduwar cutar a kasar nan.
A ranar Alhamis mutum 558 ne suka kamu kuma mutum biyu sun mutu a kasar nan.
Hukumar NCDC ta ce an gano wadannan mutane a jihohi 15 da Abuja a kasar nan.
Mutum 376 sun kamu a jihar Legas, Oyo-33, Akwa-ibom-26, Abuja -22, Imo-15, Bayelsa-13, Ekiti-13, Kano-12, Ogun-11, Filato-11, Delta-9, Jigawa-6, Rivers-4 da Zamfara-4.
A ranar Juma’a mutum 590 ne suka kamu samman mutum takwas sun mutu a jihohi 17 da Abuja.
Legas- 308, Akwa-ibom-54, Katsina -40, Oyo-39, Rivers -26, Neja-23, Gombe-19, Ogun-16, Ekiti-15, Abuja-10, Nasarawa-10, Delta-9, Bayelsa-5, Filato-5, Imo-4, Ebonyi-3, Jigawa-3 da Kano -1.
Zuwa yanzu mutum 173,411 ne suka kamu, mutum 2,149 suka mutu a kasar nan.
An sallami mutum 164,978 a kasar nan.
Gargaɗin kwamitin PSC
Domin hana gwamnati kara saka dokar zaman gida dole shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar korona Boss Mustapha ya yi kira ga mutane da kada su yi wasa da kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar da gwamnati ta saka.
A ranar Juma’a kwamitin ta kuma gargaɗi jami’iyyu da hukumar zabe da su rage yin taruka ba tare da ana kiyaye dokokin gujewa kamuwa da korona a kasar nan, wato a tabbata ana saka takunkumin fuska sannan ana bada tazara a tsakanin juna da kuma mulke hannu da da man tsaftace hannu.
Discussion about this post