Cikin awa 48 Korona ta kama mutum 429 a Najeriya, mutum biyu kuma sun rasu

0

Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 429 da suka kamu da cutar Korona kuma mutum biyu sun mutu daga ranar Lahadi zuwa Litini a Najeriya.

Hukumar ta ce an samu mutum 216 da suka kamu da cutar a jihohi biyu ranar Lahadi a kasar nan.
Jihohin Legas-108 da Akwa-ibom-96.

A ranar Litinin kuma an samu mutum 213 da suka kamu sannan mutum biyu sun mutu a jihohi 12.

Jihar Legas -157, Rivers- 20, Filato-12, Oyo-6, Enugu-6, Gombe-3, Bauchi-2, Imo-2, Kaduna-2, Edo-1, Ekiti-1 da Ogun-1.

Zuwa yanzu mutum 171,324 ne suka kamu, an sallami mutum 164,789.

Mutum 2,134 sun mutu sannan mutum 4,402 na killace a asibitin kula da masu fama da cutar a kasar nan.

Jami’an kiwon lafiya a Najeriya na fargaban sake barkewar cutar korona zango na uku a kasar nan.

Jami’an lafiyan sun fara fargaban ne tun bayan da aka samu tabbacin bullowar zazzafar nau’in cutar ‘Delta’ a kasar nan.

Tun bayan haka ne aka fara samu karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da yawan da cutar ke kashewa a kasar nan.

A dalilin haka gwamnati ke kara yin kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin kare kansu da na kusa da su daga kamuwa da cutar

Share.

game da Author