Najeriya za ta sake ciwo bashi karo na 11 daga Chana

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta sake lulawa ƙasar Chana domin ciwo bashin da za a yi wasu ayyukan titinan jiragen ƙasa a wasu sassan ƙasar nan.

Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Ameachi ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a ARISE TV da safe.

Amaechi dai kenan ya yi baki-biyu, domin a makon da ya gabata cewa ya yi a Standard Chartered Bank za a ciwo bashin, ba daga Chana ba.

Haka kuma Amaechi bai bayyana adadin yawan kuɗaɗen da za a ciwo bashin ba. Amma dai ya ce ana nan ana tattaunawa.

Ɗanyen Nama Ba Ya Kashe Kura:

Ya zuwa watan Maris dai an ciwo bashi sau 11 a ƙasar Chana, tun daga 2010 zuwa yau.

Idan Najeriya ta sake ciwo wannan bashi, adadin bashin da ake bin ƙasar nan zai haura dala biliyan 87.2 da ake bin Najeriya a yanzu.

Amaechi ya bayyana cewa tuni an fara biyan bashin aikin titin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.

“Dala miliyan 500 aka ciwo aka yi aikin. Amma zuwa yanzu har an biya dala miliyan 150. Inji Amaechi.

“A baya Naira miliyan 70 kaɗai ake tarawa a duk wata a jigilar fasinja zuwa Abuja daga Kaduna. Amma a yanzu ana iya tara har Naira miliyan 350 a wata.” Inji Amaechi.

Share.

game da Author