Samun ilimi da wuri shine zai magance yada bayanan karairayi a Najeriya – In ji Babban Darektar OSIWA

0

Babbar darektar shirin tabbatar da al’ummar da ba ta kyamar ra’ayoyi ko al’adu mabanbanta a yankin Yammacin Afirka wato Open Society Initiative for West Africa OSIWA a turance, Madam Aysha Osori ta ce samar da illimin farko mai nagarta shi ne zai fi tasiri wajen shawo kan matsalar yaduwar bayanai marasa gaskiya da masu yaudarar jama’a a Najeriya.

Madam Osori ta bayyana haka ne a jawabinta na bude taro a Kwame Karikari Fact-Checking and Research Fellowship, ko kuma shirin hadakar bincike da duba gaskiya ta Kwame Karikari, inda ta ce koya wa yara kanana yadda zasu dauki dabi’ar tambaya zai samar da al’adar binciken gaskiyar batutuwa tun daga farkon rayuwarsu.

Hadakar binciken wadda ta cika shekaru uku da kafuwa yanzu tana daya daga cikin shiriye-shiryen DUBAWA a karkashin Premium Times Centre for Investigative Journalism (PTCIJ)

Lauyar kuma mai bayar da shawara kan dabarun sadarwa ta ce ya kamata a sanya wani tsari na binciken gaskiya a cikin shirin koyarwar makarantu. Wannan zai taimaki yara wajen tantance farillan gane gaskiya wanda kuma zai taimaka musu wajen tantance duk wani bayani da suka samu nan gaba.

“Duk wadannan batutuwa, abubuwa ne da illimi mai nagarta kadai zai iya kawar da su, kuma wannan na daya daga cikin dalilan da suka kawo ku nan…. Tana magana da daluban da suka zo karbar horaswa dangane da mahimmancin duba gaskiyar. “A illimantar da yara dan ya taimaka musu wajen fahimtar gaskiyar lamura, su kuma rika yin irin tambayoyin da ku kanku manya za ku yi. Misali, shin wannan gaskiya ne, wannan dai dai yake? Zan iya tantancewa? labarin yana da kan gado…?

Ta kuma bukaci daliban da su rika duba gaskiya ta yadda zai tabbatar da dorewar dimokiradiyya wadda ta ce a yanzu haka tana fama da kalubalen bayanai na karya da masu yaudarar jama’a.

“Bayanai marasa gaskiya na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen rage kimar cibiyoyin da ke wanzar da dimokiradiyya, sauya halayyan masu zabe, amfani da banbance-banbancen jama’a da rashin tsaro wajen haddasa rashin jituwa tsakanin al’umma. Yanzu da dimokiradiyya ke samun karbuwa a kasashen duniya, muna tsakiyar yanayin da ke janyo koma-baya. Muna sane da cewa hakan zai sauya har a kai ga samun cigaba, amma kafin ya sauya, ya kamata mu yi duk abun da zamu iya yi.”

Hadakar binciken ta Dubawa 2021 wadda aka rada wa suna Kwane Karikari Fact Checking and Research Fellowship dan karrama tsohon Farfesan Ghana mai suna Kwame Karikari yana a karo na uku ke nan bayan da aka kaddamar da shi a shekarar 2019

Hadakar binciken na bana ya sami halartar dalibai 26 wadanda ake sa ran za su taimaka wajen yakar bayanai marasa gaskiya a yankin. Daliban sun fito daga kasashen da suka hada da Najeriya, Ghana, Saliyo, Gambiya da Liberiya.

Share.

game da Author