Ba zan koma APC ranar 12 ga Yuni ba – Inji Gwamna Matawalle

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ƙaryata labaran da ake ta yadawa wai zai canja sheka daga PDP ya koma APC ranar 12 ga Yuni.

Matawalle ya ce bai faɗi haka kuma ma hakan baya cikin lissafin sa a yanzu.

Game da korar kwamishinoni da yayi ya ce babu abinda ya haɗa hakan da wani shiri wai nasa na komawa wata jam’iyya.

” Na shekara biyu kenan a kan mulki, saura shekara biyu wa’adin zango na na ɗaya ya cika, saboda haka sai naga ya kamata in yi irin wannan tankaɗe da rairaya, wato in yi garambawul domin kuma mu tsara yadda za mu tunkari shekaru biyun da suka rage mana masu zuwa.

Da aka tambaye shi ko akwai wani tattaunawa da yake yi da wasu kan yiwuwar canja sheka, ya ce ” Tattaunawa a wurin ɗan siyasa ai ya zama dole, tattaunawa kamar da ƴan siyasa, abokan ka, mutane da talakawan ka duk dole ka riƙa tattaunawa da su, ni irin wannan tattaunawa na ke yi.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wata majiya da ke kusa da gwamna Matawalle ya gaya mata cewa gwamnan zai canja sheka ranar 12 ga Yuni.

Majiyar ta shida wa jaridar cewa shirye-shiryen canja jam’iyyar ne ya sa gwamnan ya kori manyan ma’aikatan da ya nada shekaru biyu da suka wuce, wato a lokacin da ya zama gwamna.

Share.

game da Author