APC Ta sha kashi a zaben cike gurbin kujerar ɗan majalisa na Sabon Garin Zaria

0

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna ta kwashi kashinta a hannu a zaben cike gurbin kujerar ɗana majalisar jama’ar har Kaduna da aka yi ranar Asabar.

Duk da ko cewa jam’iyyar ce mai mulki a jihar Kaduna kuma kujerar ɗan majalisan da aka sake zabe akai jam’iyyar APC ce ke rike da ita kafin majalisa ta kori dan majalisan da ke wakiltar Sabon Gari a majalisar wanda tsohon shugaban majalisar jihar ne.

Idan ba a manta ba ɗan majalisa Aminu Shagali dake wakiltar Sabon Garin Zaria ne yake akan kujerar, sai dai kuma tun bayan tsige shi da aka yi a majalisar aka naɗa Yusuf Zailani, ya yi watsi da ayyukan majalisar a cewar majalisar.

A dalilin haka, a watan Afrilu, majalisar ta sanar da korar sa daga majalisar da kuma sanar da kujerar sa babu kowa

Hukumar zaɓe za gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Sabon Gari da ke Zariya sai dai kuma sakamakon Zaɓen ya baiwa jam’iyyar APC kunya domin jam’iyyar adawa ce ta yi nasara a zaben.

Dakta Muhammed Musana hukumar Zaɓe ta Kasa wanda shine malamin zaben, ya bayyana sakamakon zaben kamar haka:

Musa Musa na APC – 7,404, Usman Baba na PDP – 9,113, Anas Abdullahi na ADC – 62; Chindo Ibrahim na ADP – 61, Musa Halilu na PRP – 305.

Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero ya ce wannan nuni ne cewa ƴan Kaduna sun gaji da jam’iyyar APC a jihar

Share.

game da Author