SHUGABANCIN APC: Takara Tsakanin ‘Mai Auri-saki, Mai Auren-jari, Mijin-ta-ce, Ta-more-miji da Masu Jiran ‘Yar-sadaka’

0

Bayan an raba auren jam’iyyar APC da Adams Oshimhole, wanda ya kasance surikin da ya riƙa rigima da dangin matar sa APC na uwa da na uba, an tura jam’iyyar a gidan Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala-Buni, domin ta yi zawarcin watanni shida kafin a samu bazawarin da ya dace a sake ɗaura mata aure.

Sai dai kuma rigingimu da algungumancin da Oshimhole ya haddasa tsakanin ‘yan uwan APC sun zama ƙarfen-ƙafan da har yau Mala-Buni bai ƙarasa sasantawa ba, ta yadda ko da an sake ɗauka wa APC aure, to kamata ya yi a samu haɗin kai tsakanin dangin uwa da ɓangaren dangin uba, yadda za su ɗunguma tare zuwa rakiyar amarya gidan miji.

Bayan tsawon lokacin da APC ta yi a hannun Mai Mala-Buni ta na zawarci, yanzu dai an samu zawarawa da samari har su takwas da su ka fito neman auren ta.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bi diddigin manema auren APC domin masu karatu ya san su tun kafin ranar ɗaurin aure ta zo.

Daga Manema Auren APC Su Ka Fito?:

Da yake ana sa ran ɗan takarar shugabancin ƙasar nan na APC a 2023, daga kudancin Najeriya zai fito, sai uwar jam’iyyar ta miƙa shugabancin jam’iyya ga Arewacin Najeriya.

Salihu Mustapha dai shi ya fara fitowa neman shugabancin jam’iyya. Sannan akwai Sanata Tanko Almakura, tsohon gwamna a Jihar Nassarawa. Sai tsoffin gwamnonin Jihar Barno biyu, Kashim Shettima da Ali Modu Sheriff. Ga kuma Sanata Ɗanjuma Goje, Abdulaziz Yari, Ibrahim Baba, Sunny Moniedafe daga Jihar Adamawa.

Waɗannan su ne za su yi takarar shugabancin APC, jam’iyyar da aka kafa cikin watan Fabrairu, 2013 bayan an yi gamin-gambizar jam’iyyu uku sun haɗe wuri ɗaya, wato ACN, CPC da ANPP.

APC ta yi shugabanni uku a baya, amma biyu daga cikin su auren rabuwa aka yi baram-baram.

John Odigie-Oyegun ya gaji Shugaban Riƙo na farko, Bisi Akande. An tilasta shi sauka aka naɗa Adams Oshimhole a Taron Gangami na watan Yuni, 2018.

Oshimhole ya yi shekaru biyu kacal, inda cikin watan Yuni 2020 aka tumɓuke shi ana miƙa APC riƙo a hannun Mai Mala-Buni.

Sashe na 17(i) na Kundin Dokokin APC ya nuna cewa zangon shekaru huɗu (4) ne wa’adin shugabannin jam’iyya za su yi. Amma su na da ‘yancin sake tsayawa zango na biyu na wasu shekarun huɗu.

Oshimhole zai iya neman tsayawa sake shugabanci. Amma idan ɗan kudu ne zai tsaya wa APC takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, to ba ma za a sa Oshimhole cikin masu neman takara ba.

Tanko Al-Makura: A yanzu sanata ne, kuma a baya ya yi gwamna a Jihar Nassarawa tsawon shekaru takwas. Tun cikin watan Maris, 2021 ya fara kamfen na neman shugabancin jam’iyyar APC.

An riƙa watsa kamfen ɗin sa a gidajen radiyo kuma ana ganin fastocin hotunan sa. Haka nan kuma ana watsa saƙonnin taya shi kamfen a soshiyal midiya.

“Idan aka jefo takarar shugabancin APC zuwa shiyyar Arewa ta Tsakiya, to zan fito takara. Amma idan aka ce sai ɗan Arewa maso Gabas ko Arewa maso Yamma, to zan haƙura, saboda ni mutum ne mai biyayya ga jam’iyya.” Inji Al-Makura cikin watan Mayu.

Idan Al-Makura ya yi nasara, zai zama shugaban APC na farko daga ɓangaren CPC. Dama kuma shi kaɗai ne wanda ya taɓa yin gwamna a lokacin da Buhari ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin CPC, a zaɓen 2011.

Al-Makura na cikin waɗanda su ka kafa jam’iyyar PDP. Ya shiga CPC cikin 2011, kuma ya ci zaɓen Gwamnan Jihar Nassarawa.

Ɗanjuma Goje: Shi ma tsohon gwamna ne a Jihar Gombe har tsawon shekaru takwas a ƙarƙashin PDP. Wannan ne zangon sa na uku a matsayin Sanata zango ɗaya a PDP, zango biyu kuma a APC.

Goje ya nemi tsayawa takarar Shugaban Majalisar Dattawa bayan zaɓen 2021. Amma an matsa masa lamba ya janye an zaɓi Ahmad Lawan.

Kamar Al-Makura, shi ma Goje ya na da goyon bayan Gwamnan Jihar sa, Muhammad Yahaya.

Wasu na ganin idan Goje ya zama shugaban PDP, to zai iya maido gungun nPDP da su ka fice daga APC a fusace, bayan “an ci amanar su”,

Ali Modu Sheriff: Shi ma ya yi Gwamnan Jihar Barno tsawon shekaru takwas a ƙarƙashin ANPP a zaɓen 2003, inda ya doke Mala Kachalla.

Kafin lokacin kuma ya yi Sanata a zaɓen 1999, a ƙarƙashin jam’iyyar APP.

Sheriff, wato SAS, ya samu matsala da gwamnan da ya gaje shi, wato Kashim Shettima. Da farko dai ba Shettima ne ya tsaya takarar gwamna ba. Shettima ya zama ɗan takara, bayan dan takarar da Sheriff ya tsayar Boko Haram sun kashe shi.

Sheriff ya koma PDP har ya zama shugaban jam’iyyar, bayan ta faɗi zaɓen 2015.

Sheriff ya riƙa samun matsaloli bayan da wani Baturen Austaraliya mai shiga tsakani wajen karɓo waɗanda Boko Haram su ka yi garkuwa da su, ya zarge shi da ɗaukar nauyin Boko Haram.

Sheriff dai a yanzu ya na ganin matsawar aka miƙa takarar shugabancin APC a Arewa maso Gabas, to bai ga abin da ke iya hana shi samun nasara ba.

An sha ganin ya na kai ziyara wurin Shugaban Riƙon APC na yanzu, Mala-Buni tsohon abokin sa.

Sai dai kuma akwai gagarimar matsala a gaban sa, domin shi ma Kashim Shettima ya fito takara.

Kashim Shettima: Majiyoyi da dama daga cikin APC sun tabbatar cewa Kashim Shettima shi ma ya na zawarcin kujerar shugaban APC.

Sanata Shettima kamar Sheriff, ya yi gwamna a Barno shekaru takwas. Shi ne ma ya hau kujerar bayan saukar Sheriff.

Ya shafe shekaru takwas cur ya na fama da Boko Haram, har ta kai ga sun kafa tutoci a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Sai dai kuma jama’a da dama sun yaba irin ƙoƙarin da ya yi wa Jihar Barno. Duk da cewa ana muzuru ana shaho a jihar Barno, hakan bai hana Shettima samar da ayyukan inganta rayuwar jama’a ba.

Ya taɓa zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, abin da ake ganin hakan zai iya taimaka masa wajen samun goyon bayan wasu gwamnoni daga Arewacin Najeriya.

Sannan kuma tabbas Gwamna Babagana Zulum zai goyi bayan sa, ba Ali Modu Sheriff zai mara wa baya ba.

Abdulaziz Yari: Shi dai Tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari tun cikin Satumba, 2020 ya fara nuna maitar sha’awar shugabancin APC.

“Ai na sha furta cewa tun daga sama har ƙasa na san yadda ake zaɓen shugaban jam’iyya a APC, PDP, CPC.”

Yari zai iya samun matsala, domin shi ne ya haddasa wa APC yin asarar kujerar gwamna, sanatoci da mambobin majalisar tarayya baki ɗaya a jihar Zamfara.

Shi ya haddasa rikicin da INEC ta hana APC shiga zaɓen 2021 a Jihar Zamfara. Kamar yadda ta hana APC shiga zaɓen na 2021 a jihar Ribas.

Ana ganin idan ma ya zama shugaban jam’iyya, zai ruɓanya irin harigidon da ya yi har ya janyo wa APC asarar jihar Zamfara baki ɗaya.

Sannan kuma a halin yanzu EFCC ta matsa masa lamba wajen binciken karkatar da maƙudan kuɗaɗen da hukumar ke zargin ya waske da su.

Sauran Samarin Da Ke Jiran ‘Sakin-wawa’:

Baya ga gingima-gingiman zawarawa irin su Sanata Goje da gudurmutsen ƙaron bazawari irin Modu Sheriff da tsoffin gwauraye su Al-Makura da Shettima da Yari, akwai irin su Salihu Mustapha daga jihar Kwara, ɗan shekara 49. Sai Ibrahim Baba daga Jihar Bauchi, wanda tsohon Ɗan Majalisar Tarayya ne. A yanzu Mashawarci ne ga Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.

Sannan akwai kuma Sunny Moniedafe daga Jihar Adamawa, wanda kowa ya san ra’ayin riƙau ɗin tafiyar gidan siyasar Bola Tinubu ne.

Share.

game da Author