A bincike musabbabin hatsarin jirgin da ya kashe COAS, Janar Attahiru – Majalisar Tarayya

0

Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Tarayya, Ndudi Elumelu, ya yi kira da a gaggauta gudanar da binciken ba-sani-ba sabo, domin a gano musabbabin hatsarin jirgin soja wanda ya gi sanadiyyar rasuwar Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.

Attahiru ya rasu tare da wasu manyan hafsoshin sojoji da kuma matukan jirgin baki daya a ranar Juma’a, a Kaduna.

Elumelu ya ce a yi binciken kwakwaf domin a gano musabbabin mutuwar Janar Attahiru, sannan kuma a binciki dalilin faduwar jiragen soja cikin shekarar nan a Abuja da kuma Barno.

“Mu marasa rinjaye mun damu kwarai da irin yadda ake samun yawan hatsurran jiragen sojoji da ake yi a kasar nan.

“Mu na kuma kira ga sojoji su ci gaba da aiki tukuru, kada abin da ya faru da su ya kashe masu guyawu.” Inji Elumelu a madadin sauran ‘yan majalisa marasa rinjaye.

Cikin watan Fabrairu jirgin sojoji samfurin Jet King Air 350 ya fado kasa a kusa da Abuja, lokacin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa Jihar Neja. Matukan jirgin bakwai duk sun mutu.

Sai kuma cikin watan Maris, wani jirgin yaki Alpha Jet ya bace a Barno a lokacin da ya ke kai wa Boko Haram farmaki. Matukan jirgin biyu sun mutu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Majalisar Tarayya za ta binciki Max Air da Aero Contractors.

Majalisar Tarayya ta amince ta binciki zargin sakaci da ake yi wa kamfanin zirga-zirgar jirage na Max Air da Aero Contractors.

Hakan ya biyo bayan wani korafi da Dan Majalisar Tarayya Umar Balla daga Jihar Kano ya yi a ranar Laraba a majalisa.

Bala, dan APC daga Kano, ya nemi a binciki Max Air da Aero Contractors, domin a gano ko akwai sakaci a wasu lamarin da su ka faru a jiragen biyu kwanan nan.

Balla ya bada labarin yadda jjrgin Max Air dauke da Sarkin Kano da sauran fasinjoji 139 su ka tsallake rijiya, inda bayan jirgin ya tashi minti 10 daga Kano zuwa Abuja, ya karkata, ya koma Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin ya koma ne bayan ya yi karo da wani tsuntsun da ya kutsa cikin injin jirgin guda daya.

“Haka kuma wasu mutum 90 sun tsallake rijiya a cikin jirgin Aero Contractors. Sannan kuma tsuntsu ya yi karo da jirgi kirar Boeing 737, tilas ya koma Kano a kan hanyar sa ta zuwa Abuja. Ya kamata a bincika ko akwai sakaci.

Hakan ya faru bayan yawan samun hadurran jiragen yaki na soja a baya, cikin wannan shekarar.

Bayan Majalisa ta amince da a yi binciken, an umarci Kwamitin Lura da Tashoshin Jiragen Sama ya gudanar da bincike kan kamfanonin jiragen Max Air da Aero Contractors.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wadansu tsuntsaye su ka tilasta wa jirgi dauke da Sarkin Kano juyawa ya yi saukar gaggawa a Kano.

A ranar Talata ce jirgin sama na kamfanin Max Air dauke da Sarkin Kano Aminu Ado-Bayaro, ya yi saukar gaggawa, minti 10 kacal bayan tashin sa daga filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA).

Jirgin mai lamba VM1645, ya na dauke da fasinjoji da dama baya ga Sarkin Kano a ciki. An shirya jirgin zai tashi da karfe 1:30 na rana, amma aka samu jinkiri na mintina 30.

An ruwaito cewa minti 10 bayan jirgin ya cira sama, ya fara tangal-tangal, amma ya samu nasarar juyawa baya, ya koma filin jirgin Kano ya sauka.

Sai dai kuma Daraktan Kula da Lafiyar Jirage na Max Air, Muhammad Mubaraq ya karyata rahotannin da wasu jaridu su ka ce injin jirgin ne ya samu matsala a sama. Kuma ya ce karya ce, babu wanda ya kusa mutuwa a cikin jirgin.

“Tsuntsaye ne aka samu akasi su ka kutsa cikin injin jirgin. Kuma wannan ba wani abin tayar da hankali ba ne, domin matukin jirgin ya bi ka’idojin da aka shimfida. Wato idan haka ta faru, ya koma inda ya fito idan ya fi masa kusa.” Inji Mubaraq.

“Yanzu haka jirgin tuni an gama duba lafiyar sa, har ya tafi Abuja daga Kano. Saboda haka ba daidai ba ne a rika cewa jirgin ya kusa rikitowa ya kashe mutanen da ke cikin sa.

“Kuma su tsuntsaye ai sun saba yi wa jirage cikas bayan jiragen sun tashi sama.”

Share.

game da Author