Gwamnan Sule na jihar Nasarawa ya siya wa sarakunan jihar motocin kasaita na biliyoyin naira

0

Kowa dai da abin da ya dame shi. A daidai gwamnatin Kaduna na fama da karauniyar rage ma’aikata don ta samu kudin gina tituna da kirkiro hanyoyin tara kudade a jihohi da gwamnatoci ke yi, A jihar Nasarawa kuwa watandan motocin kasaita gwamnan jihar Abdullahi Suke ya yi wa manyan sarakunan jihar.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa gwamnan ya siya wa manyan sarakuna kalla 26 motocin kasaita wanda kudaden su kan fara ne daga naira miliyan 50 zuwa sama ne.

Gwamnatin jihar ta koka kan karancin kudade musamman wadanda za a rika biyan kudaden ma’aikatan jihar.

Masu yin fashin baki a harkar siyasa da tattalin arziki sun ce wannan ba lokaci bane na kashe irin wadannan kudade don faranta wa sarakuna rai haka kawai da motoci masu tsada irin haka.

” Jihar Nasarawa na daga cikin jihohin kasar nan da ke samun mafi karancin kudaden shiga harda na kaso daga gwamnatin tarayya. Idan har gwamna zai iya dibar tsabar kudi irin haka ya siya wa sarakuna motoci, tabbas bai yi nazari mai zurfi ba.

” Kamata ya yi idan ma babu abinda za ayi da su ne a ajiye su domin bacin rana. Idan kuma dole sai an siya wa sarakunan motoci akwai motoci na daidai kima, wanda a ganina ma ba abu ne da ake bukata kashe wa kudi irin haka ba.”

Share.

game da Author