HARAMTA KIWON SHANU: Audu Ogbeh ya goyi bayan gwamnonin kudu 17

0

Tsohon Ministan Harkokin Noma, Audu Ogbeh ya bayyana goyon bayan sa ga haramta kiwon shanu da karakainar makiyaya daga Arewa zuwa jihohin kudu 17 na kasar nan.

Kwanan baya ne Gwamnoni 17 na Kudu su ka zartas da kudiriri 12, ciki har da haramta karakainar Fulani makiyaya zuwa kudancin kasar nan, bisa dalilin haddasa fadace-fadace da kashe-kashe da barnata dukiyoyin da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma.

Gwamnonin sun ce dandazon Fulani makiyaya a yankunan su na kara haifar da matsalar tsaro da tashe-tashen hankula a jihohin su.

Da ya ke bayani, Audu Ogbeh wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (ACF), a ranar Talata ya ce hana kiwon shanu da gwamnonin kudu 17 su ka yi daidai ne, domin zai hana kutsen makiyaya masu dauke da muggan makamai da ke kwararowa daga kasashen da ke makautaka da Najeriya.

“Wato su wadannan makiyaya fa imanin cikin zuciyar su na kakkake masu cewa babu wani aibi don sun banka dabbobin su ko a gonar wa su ka ga dama. Gani su ke yi daidai ne idan sun cinye amfanin gonar da su ka ga dama. Kuma gani su ke yi za su iya yi wa kowace mace fyade, kuma su kashe wanda ya yi masu tsaurin-ido. To a gaskiya duk al’ummar da ta san ciwon kan ta, ba za ta lamunci wannan rashin mutuncin ba.” Inji Audu Ogbeh.

Ogbeh wanda ya yi Ministan Gona daga 2015 zuwa 2019, ya ce hare-haren Fulani makiyaya a yankin kudu ne ya haifar da tashin farashin garin kwaki.

Sai dai kuma ya kara da cewa idan ba a bi shawarar Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje wanda ya ce a hana makiyaya kwararowa daga makautan kasashe ba, to ba za a iya magance matsalar makiyaya a fadin kasar nan ba.

Audu Ogbeh ya nemi Najeriya ta shiga gaba ta tabbatar an yi wa Dokar Sharadi na 3 na ECOWAS kwaskwarima.

Dokar dai ta amince makiyaya su rika karakaina da shanu a fadin kasashen ECOWAS.

Share.

game da Author