Allah Ya zagayo da mu wannan shekara, kuma cikin wata na tara a kalandar Musulunci, watan da Allah (S.W.T) Ya saukar da littafi mai tsarki, wato Alkur’ani mai girma. Shi ne watan kasafi, watan ibadar bayin Allah, watan addu’a da neman gafara a wajen mai duka, watan yawaita karatun Alkur’ani Mai Tsarki, watan dagewa da bautar Allah da koma wa gareShi baki daya, kuma watan rahama da gafara.
Mun shiga watan Ramadan har tafiya ta fara nisa, domin yau goma ga wata, watan da Manzon Allah (S.A.W) ya ke cewa ga wata nan mai alheri an danno kanku domin ya yi muku inuwa.
Manzon Allah ya umarce mu da mu dunga yin shiri a duk shekara domin tarbar wannan wata mai alfarma da daraja.
Kowanne yini na wannan wata akalla darajarsa a wajen Allah ta kai kwana sittin, haka kuma kowanne dare shi ma darajarsa ta kai kwana sittin a wajen Allah madaukaki.
Wato idan mutum ya yi ibada a kowanne yini na wannan wata, ya yi ibadar kwana sittin kenan, hakazalika in mutum ya yi ibada a kowanne dare na watan ya yi ibadar kwana sittin kenan. Wannan ya na kwadaita mana cewa idan mutum ya yi ibada a kowanne yini na Ramadan to ya yi ibadar wata biyu kenan. Sannan idan mutum ya yi ibada a kowanne dare na Ramadan shi ma ya yi ibada ta wata biyu kenan.
Kenan in mu ka yi ibada dare da rana a cikin watan Ramadan, mun yi ibadar kusan kwanaki dubu uku da dari shida (3600 days) a cikin kwanaki talatin (30 days) kacal. Wato ibadar shekara goma kenan (10 years) a cikin wata daya. Hakika wannan gara6asa tana da yawa sosai.
A cikin watan akwai wani dare da darajarsa tafi wata dubu, wato, fiye da shekara taminin (80 years) kenan. Wannan dare shi ne…LAI LATUL QADR.
Wannan yana kwadaitar da mu cewa in mu ka dage daga farkon watan Ramadan zuwa karshen sa za mu iya yin ibadar fiye da shekara casa’in (90 years), kun ga kenan kusan za mu iya kamo mutanen baya da suka yi shekaru dubbai a baya suna bautar Allah.
Yan uwa zuciya ita ce kwaryar kar6ar duk wani aikin alheri da ke cikin wannan wata, don haka kowa ya wanke zuciyarsa ya tari wannan gagarumin aikin alkhari.
Gyaran zuciya shi ne mutum ya wanke ta sarai kar ya bar lam’a ko daya domin ya rabauta da garabasar dake tattare a cikin wannan wata.
Mata sai sun wanke kwanuka sun fita sun yi kal-kal, sannan suke zuba abinci a ciki, domin kar su zuba abincin a cikin kwano mai datti shi ma abincin ya yi datti, duk saboda alfarma wannan wata.
Shi ya sa ka ke ganin ilimi yana shiga zuciyoyin mutane lokaci daya, amma in ya tashi fitowa sai ya fito iri daban-daban ko da kuwa a yayin yin jarabawa ne.
Idan ilimi ya shiga zuciya mai kyau to in tashi fitowa sai ya fito lafiya kalau babu wata miskila ko tangarda. Amma in ya samu najasa ta hanyar gur6acewa da wani abu marar kyau to sai ka ga an samu matsala.
Gyaran zuciyar mu shi ne mu yawaita bautar Allah ta hanyar sallolin farilla da nafilfuli da yawan yin istigifari da yawaita salatin Annabi da hailala da karatun Alkur’ani. Wadannan sune abubuwan da za mu ci gaba da yi har karshen wannan wata da bayansa.
A cikin wannan dare da darajarsa tafi shekara taminin (80 years), Allah Ya ke yin kasafin (budget) ni’imar da zai saukar a wannan shekara. Ni’ima ta dukiya da ‘ya’ya da abinci da ta duniya, yawan ruwan da za a samu a shekarar tare da yawan mutanen da za su mutu a wannan shekara.
A cikin shi wannan dare na LAI LATUL QADR ake mika wa mala’iku, wato (muwakkaluna) kundin aikinsu na wata shekara domin aiwatarwa, kwatankwacin yadda shugabannin mu suke yi a wannan duniya wajen kasafin kudi.
A karshe ina yi mana addu’ar Allah Ya ba mu ikon dagewa da ibada gareShi. Ya ba mu kwarin gwiwar ci gaba da yin aiyukan alheri a cikin wannan wata. Ya ba mu ladan Azumi cikakke. Allah Ya sa mu dace da ganin wannan dare na LAI LATUL QADR, Ya sanya mu cikin bayin Sa da zai ‘yan ta a cikin wannan wata.
Ameen summa Ameen.
Muazu Dan Jarida ne dake aiki da Freedom Radio, Kano
08036433199
muazumj@gmail.com
Discussion about this post