Majalisar Dattawa ta amince Shugaba Muhammdu Buhari ya sake tattago bashin dala biliyan 1.5 da kuma kari wasu fam na Ingila miliyan 995.
Wannan amincewa ta biyo bayan Rahoton Kwamitin Basussukan Cikin Gida da na Waje na Majalisar Dattawa ya gabatar, karkashin Shugaban Kwamitin, Clifford Odia, dan PDP daga mazabar Edo ta Tsakiya.
Cikin watan Mayu 2020 ne Shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa wasikar neman amincewa a ciwo bashin, domin a samu damar cike gibin da kasafin kudi na shekarar2020 ya samar, domin a yi manyan ayyukan raya kasa da kudaden, a dukkan fadin kasar nan.
“Gwamnatin Tarayya ta ce wannan bashi dai za ta yi amfani da kudaden wajen yin ayyukan raya kasa, sannan kuma a samu damar habbaka jihohi domin a samun hanyoyin kara wa tattalin arzikin Najeriya bugun numfashi mai karfi.”
Da ya ke gabatar da rahoton a gaban majalisa, Sanata Ordia ya yi tsinkayen cewa basussukan da za a karbo ba masu tare da karfen-kafa ba ne, basussuka ne da kamfanoni za su yi wasu ayyuka da kudaden su, sannan daga bisani su rika cire kudaden su da ribar su.
Ordia ya kara da cewa basussukan kuma ba su da kudin ruwa masu yawa, sannan kuma akwai ratar isasshen lokacin biya da fara biyan bashin kudaden idan aka bayar da bashin.
“Wannan bashi zai kasance abin alheri ga daukacin ‘yan Najeriya ta hanyar yin amfani da kudaden a gaggauta kara wa tattalin arzikin Najeriya bugu-bugun numfashi, daga halin gargarar da ya ke ciki, sanadiyayyar jijjigar da ya sha a sakamakon barkewar cutar korona a duniya.”
Za a ciwo basussukan ne daga Babban Bankin Duniya da kuma wata Cibiyar Hada-hadar Cinikayya ta Kasa da Kasa da ke kasar Brazil.