Ahmed Musa zai dan taba wasa a tsohon kulob din sa, Kano Pillars

0

Kaftin din ’yan wasan Super Eagles, Ahmed Musa na shirin karbar tayin taba wasa na wani dan takaitaccen lokaci a tsohon kulob din sa, Kano Pillar.

Wannan dai wani kokari ne domin ya jefi tsuntsu biyu da dutse daya, wato ya bunkasa wasan kwallon cikin gida Najeriya sannan kuma ya rika motsa jiki, kasancewa a yanzu ba wani kulob ya kai ga komawa ya na wasa ba tukunna.

Kafafen yada labarai da dama a Kano, ciki har da Kano Focus sun ruwaito cewa Ahmed Musa mai shekaru 28 a duniya, a yanzu a tsaye ya ke da kafafun sa a duniyar kwallo, ba a karkashin wani dillali ba, ya dan tsaya ne ya huta, sannan kuma ya darje daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin sayen sa.

An fara zawarcin sa ne bayan bayan ya bar kungiyar Al Nasar ta Saudi Arabia, cikin watan Oktoba.

Akwai kungiyoyin da ke zawarcin sa a kasashen Turkiyya, Rasha da kuma Ingila.

Sai dai kuma ya nuna cewa ya na da niyyar komawa daya daga cikin kasashen Turai a sabuwar kakar kwallon kafa mai shigowa watanni kadan masu zuwa.

Kafin ya koma Turai ne ruwayoyi su ka nuna cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Shugaban Kwallon Kafa Gasar League na Najeriya, Shehu Dikko, su ka shawarce shi ko zai dan koma tsohon kulob din sa, Kano Pillars ya dan taka leda a can, ko da na wani dan takaitaccen lokaci ne.

‘Ina Tunanin Na Dan Taba Wasa Kadan A Kano Pillars’ – Ahmed Musa

A wata gajerar tattaunawa da ya yi da Sashen Turanci na BBC Sport Africa, Ahmed Musa ya bayyana cewa, “Bayan na yi magana baki da baki da Gwamnan Kano da kuma Shugaban Kwallon LMC na Kasa, ina tunanin komawa na dan buga wasa kadan a Kano Pillars.” Inji shi.

“Zan so na ga ina yin duk wani abu da zai bunkasa wasan kwallo a Najeriya, abin da na yi a baya lokacin da ina wasa a Kano Pillars, kungiyar da na yi wa wurin zama na musamman a cikin zuciya ta.

“Kano Pillars ce ta taimaka min har aka san ni, na zama kwararre a duniyar kwallo. Don haka ni da kulob din mun zama ‘yan uwan juna kawai.”

BBC Sport Africa ta tabbatar da cewa har ma an rattaba yarjejeniyar komawar Musa Kano Pillars domin buga wasa na dan takaitaccen lokaci.

Ahmed Musa wanda ya gina katafariyar cibiyar motsa jiki a Kano domin taimakawa a bunkasa wasan kwallo daga tushe, ya ci wa Kano Pillars kwallaye 18 a kakar wasa ta 2009/2010 lokacin da ya na wasa a kulob din.

Ahmed Musa ya buga wa Najeriya wasanni 96, kuma shi ne na uku cikin ‘yan wasan da su ka fi buga wa Najeriya wasa.

Vincent Enyeama ya buga wasanni 101, Joseph Yobo wasanni 100, sai Ahmed Musa da ya buga wasanni cikon na 96, a wasan da Najeriya ta ci Lothoso 3:0 makonni biyu da su ka gabata.

Ahmed Musa ya fara buga wa Najeriya wasa tun cikin 2010.

Ya taimaki Super Eagles sun lashe Kofin Afrika cikin 2013, kuma ya buga wasanni Cin Kofin Duniya biyu da su ka gabata.

Shi ne dan wasan da ya fi ci wa Najeriya kwallaye a gasas cin kofin duniya a wasannin da ya buga a gasar ta 2014 da 2018.

Share.

game da Author