Maimartaba Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad-Sanusi, a ranar Laraba, ya karbi allurar rigakafin korona a fadarsa dake Garo a babban birnin Dutse dake Jihar Jigawa.
Sarkin yace ba kamar a baya ba da ake yada jita-jita akan rashin ingancin rigakafin allurar polio, allurar korona ta samu karbuwa a Jigawa fiye da polio.
Allurar rigakafin ta korona da polio duk suna da inganci basu da wata illa sabanin karyar da ake yadawa cewa allurar polio tana hana haihuwa, inji Maimartaba sarki.
Sarkin yace al’ummar Jigawa suna tururuwa wajen karbar allurar rigakafin korona hakan ya jawu Jihar tana kan gaba na yawan mutane a Nigeria wadanda akayi wa allurar rigakafin.
Sarkin yayi kira ga yan Jiha dasu fito su amshi allurar rigakafin korona saboda bata da illa ta samu amincewar hukumar lafiya ta duniya da gwamnatin tarayyar Nigeria.
Ba wani mutum mai hankali da zaiyi shakku kan ingancin allurar rigakafin korona saboda hukumar lafiya ta duniya ta amince da ita.
Ina farin cikin sanarwar cewa Jihar Jigawa tana kan gaba wajen yawan mutane da akayi wa allurar rigakafin korona a Nigeriya
Yace anyi masa allurar tare da iyalan gidansa da kuma sauran yan majalissarsa, yace kuwa da kuwa ya fito ya amshi allurar.
A baya Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta rawaito yadda akayi wa Sarkin Hadejia Adamu Abubakar-Maje allurar rigakafin ta korona a babbar asibitin garin ta Hadejia.