CUTAR DAJI: Zuwa asibiti da yin gwajin cutar da wuri ne mafita – In ji Dan majalisa

0

Wani dan majalisar dokoki dake wakiltan mazabar Eti-Osa a jihar Legas Gbolahan Yishawu ya yi kira ga mutane da su rika zuwa asibiti suna yin gwajin cutar daji cewa yin haka zai taimaka wajen rage yawan mutanen da cutar ke kashewa a kasar nan.

Yishawu ya yi wannan kira a taron ranar cutar daji da ake yi ranar hudu ga Fabrairu a jihar Legas.

An kebe wannan rana a kowace shekara domin wayar da kan mutane game da cutar sannan da hanyoyin gujewa kamuwa da ita.

Yishawu ya ce sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya WHO ta yi ya nuna cewa cutar daji ce cuta ta biyu dake kisan mutane a duniya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa cutar ta yi ajalin mutum miliyan 9.6 a shekarar 2018 a Najeriya sannan kuma cutar na yin ajalin mutum 1 cikin mutane shida a duk shekarar.

Ya yi kira ga sassan gwamnati da su tsananta wayar da kan mutane kan cutar sannan su tsaro hanyoyin da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Taken ranar cutar na shine “Ni ne kuma zan yi” wanda ya nuna cewa dole a mike tsaye wajen ganin an yaki cutar kasar nan.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin kira da uwargidan gwamnan jihar Kebbi Zainab Bagudu ga gwamnati da a yi wani doka da zai tilasta wa mutane yin gwajin cutar daji da zarar mutum ya kai wasu shekaru a raye.

Zainab wacce ita ce mai mallakin gidauniyar ‘MedicAid Cancer Foundation’ ta bayyana cewa yin haka zai taimaka matuka wajen kawar da matsalolin da gwamnatocin tarayya da na jihohi ke fama da su a wajen kau da cutar.

Ta ce hakan zai yiwu ne idan gwamnati ta ware isassun kudade domin gina ingantattun asibitoci domin gwaji da kula da masu fama da cutar a kasar nan.

Share.

game da Author