Hukumar kiyaye hadura ta Kasa FRSC reshen jihar Bauchi ta ci taran wani direban mota kiran bus naira 26,000 a dalilin karya dokar Korona a lokacin aikin sa.
Shugaban hukumar Yusuf Abdullahi ya sanar da haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Laraba a garin Bauchi.
Abdullahi ya ce hakan da hukumar ta yi zai zama abin koyi wa sauran direbobi dake yin kunnen kashi da kiyaye dokokin guje wa kamuwa da cutar a jihar.
Ya ce bayan haka direban ya kuma karya wasu dokokin hukumar da suka hada da rashin lasisin tuki da rashin yi wa motar da rajista da sauransu.
“Burin hukumar shine ta ga ta tabbatar kowa ya bi dokokin kiyaye kai daga kamuwa da Korona a duka tashoshin motoci sannan su ma direbobi sun kiyaye dokokin domin kare jihar da fantsamar cutar.
A dalilin haka Abdullahi ya ce hukumar ba za ta yi ƙasa-ƙasa ba wajen ganin direbobi da matafiya sun kiyaye dokar a jihar.
A wannan mako PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda Mahukunta a babban birnin tarayya Abuja suka garkame shahararren kasuwar Wuse dake tsakiyar gari Abuja sabo take dokokin korona da mutane ke yi a kasuwar.
Baya ga kasuwar Wuse, gwamnati ta garkame katafaren kasuwra UTC dake Garki.
Babban dalilin da ya sa gwamnati ta garkame wadannan kasuwanni biyu kuwa shine saboda karya dokokin Korona da mutane ke yi.
Ƴan kasuwa da dama sun shaida wa wakilin mu cewa wannan hukunci da mahukunta a babban birnin tarayyar suka dauka yayi matukar tsauri. Ƴan kasuwan sun yi cincirindo a kofar shiga kasuwannin sun yi tagumi cikin damuwa