KORONA: Mutum 1,138 suka kamu ranar Laraba a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,138 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –377, FCT-172, Filato-86,Kano-84, Edo-60, Osun-47, Nasarawa-41, Imo-40, Rivers-36, Niger-32, Oyo-32, Borno-29, Kaduna-27, Delta-18, Kwara-17, Cross River-9, Ekiti-8, Bauchi-7, Ogun-7, Sokoto-6 da Bayelsa-3

Yanzu mutum 134,690 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 108,657 sun warke, 1,618 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,415 ke dauke da cutar a Najeriya.

Ranar Talata, mutum 1,634 suka kamu a Najeriya, jihohin Amanbara, Rivers, Abia, Oyo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –50,318, FCT–17,243, Filato –8,068, Kaduna–7,706, Oyo–5,582, Rivers–5,519, Edo–3,862, Ogun–3,447, Kano–3,131, Delta–2,364, Ondo–2,339, Katsina–1,864, Enugu–1,829, Kwara–2,003, Gombe–1,678, Nasarawa–1,871, Ebonyi–1,444, Osun–1,667, Abia–1,323, Bauchi–1,164, Borno-1,009, Imo–1,156, Sokoto – 756, Benue- 848, Akwa Ibom–909, Bayelsa 688, Niger–789, Adamawa–631, Anambra–1,053, Ekiti–587, Jigawa 472, Taraba 433, Kebbi 270, Yobe-241, Cross River–212, Zamfara 209, Kogi–5.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa akalla ma’aikatan lafiya 75 suka kamu da cutar Korona a makon jiya a Kasar nan.

Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya ce kamuwa da cutar da ma’aikatan lafiya ke yi ya fara zama abin damuwa matuka yanzu.

Ya ce gwamnati na kokari wajen ganin ta kare ma’aikatan lafiya matuka.

Babban kalubalen ga ma’aikatan lafiya musamman wadanda ke kula da masu fama da korona shine rashin isassun kayan kariya daga kamuwa da cutar.

Ihekweazu ya ce daga yanzu za a fara amfani da ‘Rapid Diagnostic Test Kits (RDTs)’ wajen yi wa mutane gwajin cutar a asibitoci.

Ya ce wannan dabara zai taimaka wajen kare ma’aikatan lafiya daga kamuwa da cutar.

Sannan ya kara da cewa za a fara amfani da wannan na’ura na RDTs a Abujakuma hukumar NCDC ta fara horas da wasu ma’aikatan lafiya daga asibitoci biyar a Abuja yadda za su yi amfani da RDTs din.

Daga sai ya bayan an samu kwarewar wasu sai a fara amfani da RDT’s din a sauran manyan asibitocin kasar nan.

Ihekweazu ya yi gargadi ga ma’aikatan kiwon lafiya da su rika maida hankali a aikinsu da yin kaffa-kaffa musamman idan sun hadu da wani mara lafiya dake fama da zazzabi, ciwon kirji, rashin iya numfashi da dai sauran su.

Share.

game da Author