Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump, ya bayyana cewa zai mika wa Joe Biden mulki, duk kuwa da cewa bai yarda an kayar da shi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen 2020 ba.
Cikin wata sanarwa da Trump ya fitar, wadda Gidan Radiyon BBC Hausa ya ruwaito Trump ya na cewa, “Duk da cewa kwata-kwata ban yarda da sakamakon zaben ba, amma za a mika mulki kamar yadda aka tsara ranar 20 ga watan Janairu,” Haka Trump ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya fitar da sanarwar jim kadan bayan da ‘yan majalisa masu zabe su ka jaddada nasarar Biden da kuri’u 280, shi kuma Trump ya samu 138.
“Ina kara fada za mu ci gaba da gwagwarmaya domin tabbatar da kuri’un da aka kada bisa ka’ida ne kawai za a kirga. Duk da cewa wannan ya kawo karshen shugabanci na na musamman mai cike da tarihi, amma shi ne mafarin yakin mu na kyautata Amurka.” Trump ya fadi hakan ne ya na kuma jaddada cewa an masa magudi a zaben kasar.
A ranar Alhamis din nan ce Majalisar Amurka ta tabbatar da cewa Joe Biden na Amurka ne ya lashe zaben 2020 na shugabancin kasar.
Hakan na nufin ta tabbata cewa Shugaba mai barin-gado, Donald Trump ya sha kaye.
Majalisa ta tattabar da wannan sakamako, bayan da ‘yan jagaliyar Trump su ka yi mata kutse, su ka tarwatsa zaman ta na Laraba, zaman da aka shirya domin tantance wanda ya lashe zaben.
Wannan shigar kutse da magoya bayan Trump su ka yi dai shi ne abin kunya na farko a tarihin Amurka da aka yi wanda ya tozarta bugun kirjin kare dimokradiyya da kasar ke cewa ta na yi, fiye da kowace kasa a duniya.
Akalla mutum hudu aka bada sanarwar sun mutu a harin da magoya bayan Trump su ka kai wa Majalisar Amurka, wato State Capitol a Washington, babban birnin kasar.
Zababben Shugaba Biden da sauran shugabannin duniya sun yi tir da yadda Trump ya tunzira magoya bayan sa.