Gwamnatin Zamfara ta rufe makarantun Boko 500 masu zaman kansu

0

Ma’aikatar ilimin jihar Zamfara ta rufe wasu makarantun boko masu zaman kansu guda 500 a jihar.

Kwamishinan ilimin jihar Ibrahim Abdullahi ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata a garin Zamfara yana mai cewa mahukunta za su tabbatar kowacce makaranta mai zaman kanta ta kiyaye dokokin bude makarantu irin haka kafin a bude wannan makaranta.

Kwamishina Abdullahi, ya ce gwamna Bello Matawalle ya amince a yi haka ne bayan ya lura tsarin buɗe makarantu masu zaman kansu a jihar ba a yi shi cikin tsari ba.

Ba wai mutum da ya biya naira N30,000 shikenan kawai sai ya bude makaranta ba.

Domin kawar da irin wadannan matsaloli Matawalle ya ce ya tsara kudirori wanda za su taimaka wajen baiwa ma’aikatar ilimi ikon kula da aiyukan da makarantu masu zaman kansu ke yi a jihar.

Ya ce ya aika da kudirin gyara zuwa majalisar jihar domin gyara yadda ake gudanar da ayyukan makarantun.

Abdullahi ya ce sashen kula da aiyukkan makarantun kudi dake ma’aikatar ilimi yanzu ya zama fannin mai zaman kan sa domin gwamnati kula da aiyukan makarantun a jihar.

Share.

game da Author