KORONA: An samu karin mutum 1270 da suka kamu a Najeriya ranar Talata

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1270 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –435, FCT-234, Oyo-103, Filato-86, Rivers-71, Enugu-51, Nasarawa-41, Delta-39, Edo-39, Osun-33, Niger-31, Sokoto-23, Ondo-16, Taraba-13, Ebonyi-12, Kano-10, Abia-9, Bayelsa-8, Bauchi-7, Imo-5, Katsina-3, Gombe-1

Yanzu mutum 102,106 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 81,574 sun warke, 1,373 sun rasu.Sannan zuwa yanzu mutum 19,654 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Litini, mutum 1244 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Anambara, Ondo, Rivers da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 37,310, FCT –13,807, Oyo – 4,426, Edo –3,135, Delta –2,021, Rivers 4,011, Kano –2,465, Ogun–2,700, Kaduna –5,817, Katsina -1,690, Ondo –2,006, Borno –835, Gombe –1,457, Bauchi –1,100, Ebonyi –1,159, Filato – 5,962, Enugu –1,506, Abia – 1,095, Imo –806, Jigawa –419, Kwara –1,495, Bayelsa –569, Nasarawa –1,142, Osun –1,098, Sokoto –559, Niger – 508, Akwa Ibom – 519, Benue – 601, Adamawa – 497, Anambra –433, Kebbi –223, Zamfara –159, Yobe – 207, Ekiti –443, Taraba- 239, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa ana duba yiwuwar dage ranar komawar dalibai makarantun kasar nan saboda yaduwar Korona da ya tsananta a wannan wata.

Idan ba a manta ba a watan Disamba kwamitin PTF ta bada umurnin a bude makarantun kasar nan ranar 18 ga Janairu domin yara su koma karatu.

Adamu ya ce yanzu da cutar ta sake darkakowa a kasar nan ya zama dole a sake duba yiwuwar bude makarantun saboda kada a saka yara cikin hadari.

Ya ce bayan tattaunawa da kwamitin PTF ma’aikatar ilimi za ta Kara tattaunawa da ma’aikatanta ranar Talata domin tsaida da ranar da ya fi dacewa dalibai su koma makaranta.

Share.

game da Author