Motar kwastan ta kashe dan acaba yayin da su ka bi dan sumogal din shinkafa a guje

0

Wani dan acaba mai suna Juwon Mumini ya rasa ran sa, lokacin da wata mota dauke da jami’an kwastan ta kwace ta danne shi.

Jami’an kwastan din dai sun biyo wani direba ne a sukwane, bayan da su ka yi zargin ya dauko buhunan shinkafa na sumogal.

Wannan lamari dai ya faru a kauyen Asu a ranar Laraba, cikin jihar Ogun da ke da kan iyaka da Jamhuriyar Benin.

Kauyen Asu na ikin Karamar Hukumar Obafemi Awode, Jihar Ogun.

Motar ta kwace wurin kokarin shan wata kwana, ta banke Mumini da ke tsaye a gefe.

Wakilin mu ya samu tabbatacin cewa an garzaya da Mumini asibitin domin a duba shi cikin gaggawa, amma jami’an asibitin su ka ki karbar sa.

Daga nan kuma aka sake daukar sa aka dunguma zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Abeakula. Amma su na zuwa can, aka tabbatar cewa ya mutu.

Kakakin Majallisar Jihar Ogun, Olakunle Oloumo, ya shaida wa masu zanga-zanga cewa za su binicka su gano musabbabin kisan da aka yi wa Mumini.

Kungiyar Masatan Jihar Ogun ta harzuka bisa ga wannan kisa da kwastan su ka yi wa matashi, har su ka gudanar da zanga-zanga a Majalisar Dokokin Ogun.

Yayin da kakakin jami’an kwastan na Jihar Ogun Ahmed Oloyede ya ki cewa komai, shi kuwa kakakin ‘yan sanda Abimbola Oyeyemi cewa ya na kokarin tantance abin da ya faru kafin ya sake tuntubar wakillin na mu.

Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a rufe kan iyakoki ne jami’an kwastan ke yawan harbe masu fasa-kwaurin shinkafa.

Sun sha dirka wa mai dauke da buhu uku a kan babur bindiga.

Sannan kuma ko buhu uku direba ya dauko tare da motoci, idan yak i tsayawa su kan bi shi su harbi tayar sa, motar ta yi hatsari tare da fasinjojin.

Share.

game da Author