“Su wadannan mafarauta sun san dazukan da kyau fiye ma da Boko Haram. Kuma sun san dabarun da Boko Haram ke yi sosai. Sabaoda haka idan ba mu kara masu kwarin guiwa su da ‘yan bijilante ba, to nan ba da dadewa wa ‘yan ta’adda za su mamaye garuruwan mu karkaf.”
Wasu mafarauta da ke biye da Boko Haram a guje domin su damke su, sun gamu da ajalin su yayin da su ka taka nakiya ta fashe a kan su, duk ta kashe su.
Lamarin ya faru a kauyen Kayamla, cikin Karamar Hukumar Jere, inda maotar da mafarautan ke ciki a guje ta taka nakiyar da Boko Haram su ka binne a kasa.
Wani mafarauci mai suna Gambo da ya kubuta daga harin, ya ce su 19 ne a cikin motar su samfurin Toyota, su na cikin tafiya sai su ka ji wata irin kara mai karfin gaske.
“Wannan kara da mu ka ji, tsammanin mu taya ce ta fashe. Amma sai muka ga ashe bom ne ya tashi.
“Muna kokarin canja taya sai muka ga wasu Boko Haram su na lababowa sun tunkaro mu. Sai kuwa muka bude masu wuta, a lokaci daya kuma muka rika kiran a kawo mana daukin karin dakaru. To a lkacin sai Boko Haram din su ka arce, su ka bar wani garken shanun da su ka sato.
“Lokacin da dakarun da su ka kawo mana dauki su ka iso, kuma bi Boko Haram din a guje, sun rigaya sun yi nisa. To kan hanyar su ta dawowa sai su ka hau kan wata nakiyar bom da aka binne kan hanya. Nan take ta kashe mutum tara. Wasu mutum tara kuma su ka ji rauni. Da ido na na hangi lokacin da bom ya daga motar su sama.”
Kwaminshinan Matasa na Jihar Barno ya tabbatar da harin a lokacin da ake yi wa wasu mutum bakwai jana’iza.
PREMIUM TIMES HAUSA ta kuma buga labarin yadda ’yan bindiga su ka bindige Sarkin Maharban Adamawa a dajin Kaduna.
’Yan bindigar cikin dajin Kaduna sun bindige Sarkin Maharban Adamawa a wani gumurzu da su ka yi a cikin dajin.
Majiya a cikin iyalan sa, ta tabbatar da kisan da aka yi wa Sarkin Kungiyar Maharba na Jihar Adamawa, mai suna Young Mori.
Mori na daya daga cikin maharban da su ka rika taimakon jami’an tsaro wajen fada da masu garkuwa a cikin dazukan Arewacin Najeriya.
Haka nan shi ma shugaban ayyukan gudanarwar kungiyar mafarautan mai suna Salisu Wobkenso, ya tabbatar da kisan da aka yi wa shugaban su Mori.
Ya tabbatar da cewa a dajin Kaduna aka kashe shi.
“Wannan labari ne mai dauke da bakin ciki a gare mu mafarauta. An kashe Young Mori, daya daga cikin maharban mu na jihar Adamawa. Mori wanda ya fito daga Karamar Hukumar Guyu, ya gamu da ajalin sa yayin arangama da barayin shanu a cikin dajin Kaduna.” Inji shi.
Wobkenso dai bai yi karin haske ba, amma ya ce maharban jihar sa na cike da zaman alhini da jimamin wannan babban rashi da aka yi.
“Gwarzo, Janar Young Mori ubangiji ya yi maka rahama. Ka amsa kira, ta tafi amma b aka rabu da mu ba. Domin za ka ci gaba da kasancewa cikin zukatan mu. Allah ya kyautata kabarin Zwalka Nungurau.” Inji Johnson Gwadamdi.
‘’Duniya babban fagen taka rawa ce. Ka sha fada cewa akwai matasan zaratan Lunguda wadanda su ka fi ka jarumta. To mu dai kam mun shaida ta ka jarumtar. Ka zo duniya ka taka rawar ka, kuma ka bar duniya. Ubangiji ya sanyaya kabarin babban gwarzo,’’ Addu’ar Stephen Gyand.