2020: Sojojin Najeriya sun ‘markade’ ’yan ta’adda da ’yan bindiga 2,403 – Kakakin Hukumar Tsaro

0

“Baya ga wadannan masu laifi 2,403 da aka ‘makade’, Enenche ya kara da cewa a yankin Arewa maso Yamma an kwato dabbobi 5,281 da kuma albarusai 6,951 sai kuma bindigogi 120 masu samfuri daban-daban daga yannun ’yan bindiga.

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa a cikin shekarar 2020, tsakanin ranar 18 Ga Maris zuwa 30 Ga Disamba, sojoji sun ‘markade’ tantagaryar mabarnata 2,403 a fadin kasar nan.

Kakakin Kada LLabarai na Rundunar Tsaro, John Enenche ne ya bayyana haka a Abuja.

Ya bayar da wadannan adadi a Abuja ranar ranar Alhamis, a lokacin da ya ke bayanin irin kokarin da sojojin Najeriya su ka yi wajen yakin tsaron kasar nan a tsawon wadannan watanni 10.

“Banda wadannan kuma akwai wasu ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da dama wadanda aka ‘narkar’ da su a hare-hare ta amfani da jirayen yaki.” Inji Enenche.

Ya kuma yi bayanin cewa a cikin wadannan watanni 10, sojoji sun ceto mutane 864 da aka yi garkuwa da su a jihohi daban-daban a fadin kasar nan.

Bayan Enenche ya ci gaba da lissafo kayan yakin da aka kwato daga Boko Haram da sauran kayan sata da ceto wadanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban, ya gode wa jama’a bisa hadin kai da ake ba sojoji.

Ya yi rokon cewa a rika kai rahoton duk inda aka ji bullar batagari.

A wannan lokaci an kwato litar bakin main a disal har 9, 684,797 da aka sata, amma aka kwato.

Sannan kuma an kwato kananzir lita 33,516,000.

“An kama ‘yan iska 1, 910 tare da muggan makamai da albarusai da sauran kayayyaki duk wadannan watanni 10.

“Haka kuma an kwato kayan sata har gangar danyen mai 46, 581.8 da kuma litar kananzir 22, 881,257 ta fetur.

Baya ga wadannan masu laifi 2,403 da aka ‘markade’, Enenche ya kara da cewa a yankin Arewa maso Yamma an kwato dabbobi 5,281 da kuma albarusai 6,951 sai kuma bindigogi 120 masu samfuri daban-daban daga hannun ’yan bindiga.

Da ya ke fayyace irin gagarimin aikin da aka yi a kowace shiyya, Enenche ya ce a Yankin Arewa maso Yamma an ceto mutum 455 da aka yi garkuwa da su, sannan kuma aka kashe wasu 473.

“Yayin da aka kama manyan masu garkuwa da ‘yan bindiga da masu safarar makamai da masu yi masu leken asiri har mutum 461 a yankin, an kuma samu kudi naira milyan 6, 350,550 daga hannun masu garkuwa da mutane da kuma masu yi masu leken asiri.

A yankin Arewa maso Gabas kuma ya ce an ceto mutane 200 daga hannun wadanda su ka yi garkuwa da su. Wannan inji Enenche, aiki ne na ‘Operation Lafiya Dole.’

Ya ce an kwato albarusai 1, 385 da gurneti 45 da bindigogi daban-daban har guda 95 daga hannun Boko Haram da ISWAP a cikin watanni 10.

Bayan Enenche ya ci gaba da lissafo kayan yakin da aka kwato daga Boko Haram da sauran kayan sata da ceto wadanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban, ya gode wa jama’a bisa hadin kai da ake ba sojoji.

Share.

game da Author