An cafke wasu mutum biyu da ake zargi da kashe basaraken gidan Zaki

0

Jami’an tsaro sun cafke wasu mutane biyu masu suna Gonna Maisamari da Daniel Maisamari da ake zargi da kashe basaraken gidan Zaki dake karkashin masarautar Atyap, Zangon Kataf.

Idan ba a manta ba an kashe basaraken gidan Zaki Haruna Kuye da dan sa Daniel Kure a fadar sa, inda matarsa da ‘yar sa suka tsira da rauni.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ta tabbatar da wannan kamu da jami’an tsaro su ka yi a Kaduna yana mai cewa tun bayan kisan basaraken da aka yi jami’an tasro suka fantsama farautar wadanda suka aiakata wannan mummunar abu.

” An cafke gomna da Daniel a kauyen Kampani Amawa, dake karamar hukumar Zangon Kataf. Sai dai kuma sauran wadanda ake zargin har yanzu ana neman su.

Aruwan ya kara da cewa tuni har an mika su ga rundunar ‘yan sanda domin a cigaba da bincike.

Share.

game da Author