Ba mace ba, kai ko namiji ne ya noma shinkafa har buhu 340 a kakar noma daya, to tilas a kira shi babban manomi, musamman a Jihar Kano.
To ita kuwa Binta Muktar, wata mace mai shekaru 58, da haihuwa da ke noma a Kano, ta bayyana wa wakilin mu cewa ita ba karamar mai noma na ce.
Ta kan noma har hekta 73, filayen gonakin da ta ce duk da kudaden hannun ta.
Binta na noma masara, gero da da gero da abin da ya samu. Babbar matsalar da ta fara kuka da ita a noma, ita ce harkar noma tsada gare ta, akwai kashe kudade sosai.
Hajiya Binta, ta ce ta na da ‘ya’ya biyar, kuma dan ta hudu na cikin wadanda ke taya ta kula da harkokin noma.
“Miji na tsohon ma’aikacin gwamnati ne, ban fara harkar noma ba, sai bayan da ya yi ritaya. Saboda lokacin da ya ke aiki ana yawan canja masa wurin aiki.
“Bari na yi sai da aka yi masa ritaya sannan muka koma jihar mu ne na kama harkar noma gadan-gadan.”
Binta ta ce shekara biyar kenan da ta fara harkar noma domin naman kudi da kuma hanyar samun abinci.
“Da kudi na na sayi hekta 75. Ina sayen irin shukawa daga Hukumar Binciken Kayan Gona da kuma Cibiyar Binciken Iri a Kano, wato ICRIRAL da Afrika Rice da sauran su.
Am tambaye ta ko ta na amfani da motocin noma? Sai ta ce ta na amfani da tarakta wadda kanin ta shi ma kuma manoni ke kawo mata taraktocin, somim su yi mata aiki.
“Bana ban samu damar noma hekta 73 ba, sai hekta 11 na samu, inda na noma shinkafa buhu 340.
“Kakar bana ban samu damar yin gero mai yawa ba, saboda an sheka ruwan sama sosai. Ka san shi gero ba ya son yawan ruwan sama.”
Binta ta ce ba ta taba samun matsalar ambaliya a harkar noman ta na.
An tambaye ta batun noma da rani, sai ta ce ta gina rijiyoyi bakwai a cikin makekiyar gonar ta. Shi ya sa ba ta da matsalar ruwa da rani.
“Ina adana kayan abinci da ban sayar ba, ta hanyar tsiba su kan wasu falanka. Ka san amfanin gona ba ya so ana ajiye shi a kasa, ko da a cikin buhu ya ke, sai ya nukake. Kuma ba a ajiye buhunnan jingine da bango, saboda rima.
“Na shuka itacen karo, da shi ma na yi shingen gonar baki daya.
“Batun wani tallafi ko lamuni dai ban taba samu ba. Kuma ya kamata mu rika samun tallafin ko lamunin a saukake.”
Am tambaye ko ana nuna mata bambanci a matsayin ta na mace a harkar noma? Sai Binta ta ce: “Ka ga dai ni ma ina noma karo, amma a Kungiyar Masu Noma Kwaro ma babu mace ko daya.”
Discussion about this post