Karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya koka kan yadda zazzabin lassa ke cigaba da yaduwa a kasar nan.
Ya ce zuwa yanzu ma’aikatar kiwon lafiya ta samu rahoton yaduwar cutar a wasu jihohin kasar nan.
A cikin shekarar nan mutum 1131 sun kama cutar a jihohi 27 na kasarnan.
A makonnin da suka gabata an samu karin mutum uku da suka kamu da cutar amma cikin makonni biyu bayan haka adadin yawan wadanda suka kamu ya haura zuwa 11.
Mamora ya ce kashi 1 bisa hudu na wadanda suka kamu da cutar na jihar Ondo.
Ya yi kira ga mutane da su kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da zazzabin lassa musamman yanzu da aka shiga yanayi na hunturu.
“Cutar ba zai yi ajalin mutum ba idan an gaggauta zuwa asibiti.
Zazzabin Lassa
Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.
Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.
Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.
An fara gano wannan cuta a Najeriya a shekaran 1969 a jikin wasu ma’aikatan jinya dake aikin jinkai guda uku a kauyen Lassa a jihar Barno.
Wadannan ma’aikatan jinya dai sun rasu a kauyen sannan cutar ya ci gaba da yaduwa.
A yanzu haka duk shekara sai cutar ta sake bayyana inda mutane da dama ke kamuwa kuma da dama ke rasa rayukansu a dalilin cutar.
Alamun Kamuwa da Zazzabin Lassa
Ciwon kai: Yawaita fama da ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ta kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.
Zazzabi: Za a rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum. Zazzzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.
Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo matuka. Ko ina zai rika jin ciwo yake masa. Hakan ma alama ce dake nuna an kamu da Lassa. Hakna kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.
Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.
Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci. zaka ci gaba daya baka bukatan cin wani abu duk ko da cewa zaka rika jin yunwa.
Yawan yin Bahaya: Za a yi fama da yawan shiga bandaki a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.
Yawaita Suma: Idan har mutum ya kamu da wannan cuta, za a rika yawan suma saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.
Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan abin ya fara nisa ba a duba mutum a asibiti. Hakan na nuni cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.