Hukumar hana yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa gwamnati ta samar da lambar waya da za rika tuntubar bayanan Korona kaitsaye daga hukumar.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya ce gwamnati da hadin guiwar UNICEF ne suka kirkiro wannan hikima.
Babban makasudin samar da wannan layi shine don mutane su rika samun labaran gaskiya wato sahihan labarai game da Korona.
Mutum zai aika da sakon ‘Coronavirus’ zuwa lambar 24453, daga nan za a aiko masa da sakonni game da cutar da matsayin da duniya ke ciki da kasa Najeriya.
Ihekweazu ya ce gwamnati ta fadada abin zuwa kafafen sada zumuta na Facebook da WhatsApp domin samar wa mutane bayanan cutar.
Domin shiga wannan dandali a facebook ko Kuma WhatsApp za a iya aikawa da sakon ‘Coronavirus’ zuwa ga +234 908 740 1607. Ko Kuma ta adireshin U-Report kamar haka @ureportnigeria
Wakilin asusun UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya gargadi mutane da su cigaba da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona cewa yin haka ne kadai mutum zai iya samun kariya daga cutar.
Hanyoyi 10 don gujewa kamuwa da cutar.
1. Yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu.
2. Rufe hanci da baki idan za ayi atishawa.
3. A wanke kuma a dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
4. Rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya.
5. A saka takunkumin fuska musamman idan za a fita ko Kuma Ana cikin mutane.
6. Za a iya amfani da man tsaftace hannu Idan Babu wura da sabulu domin wanke hannu.
7. A rika zama a dakin dake da iska ko Kuma fanka.
8. A rika tsaftace muhalli akai akai.
9. A rage yawan fita Idan ba ya saka dole ba.
10. A rage yawan Zama wurin da akwai chinkoson mutane.