A ranar da Gundumar Yankin Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja da kewaye ya ƙaddamar da rabon kayan tallafin korona, wanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta raba domin rage wa jama’a radadin halin da suka shiga saboda korona, wani al’amari ya faru a wurin wanda ba a saba gani ko ji ba. A nan a gaban jama’a, Karamar Ministar Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, ta roki Allah da ya tsine wa duk wanda ya boye kayan tallafi ya hana masu bukata.
Kuma ta ce Allah ya sa wadanda suka ci rabon da ya kamata su bai wa jama’a, sun ci alakakai.
Watanni shida bayan addu’ar da Minista Ramatu ta yi, sai ga shi wani dalili ya nuna yadda ake ta fasa rumbunan adana kayan abinci a jihohi da wasu wurare, ana daka wasoson kayan tallafin da aka raba a jihohi domin a raba wa jama’a, amma har yau ba a raba ba.
Bayanin da Hajiya Ramatu ta yi dai ya tabbatar da cewa Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Ruyuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta raba kayan, domin har ana tsinuwa ga duk wanda ya boye.
Sannan kalamin da Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya yi, cewa tuni Hajiya Sadiya ta bai wa Sokoto kayan tallafi, amma sun dan jinkirta rabon ne domin a raba a gaban ta, a ranar da ta kaddamar da shirin bai wa matan karkara tallafin kudade, shi ma ya nuna tabbatar fa cewa ministar ta raba kayan tallafi.
Kasancewa har yau babu wani gwamna a kasar nan da ya fito ya karyata ministar ya ce ba a bai wa jihar sa nata kason ba, ya nuna lallai ta raba kayan tun tuni. Ita da kan ta ta bayyana cewa a jihohi biyu, wato Legas da Ogun, sai kuma Abuja ne kadai ta yi rabon kayan tallafi a kan idon ta a farkon rabon kayan tallafin lokacin da ake zaman kullen korona a gida. Ta ce sauran jihohi duk gwamnonin su aka ba, domin su ne su ka san jama’ar su, kuma sun fi kusa da su.
Duk mai hankali idan ya dubi yadda aka rika zagin Hajiya Sadiya aka aibata ta saboda rabon kayan tallafin korona, zai gane cewa abin kamar wata makarkashiya ce. Su kuma jama’a da ba su fahimta ba sai suka shiga zugar masu aibata ta, ya kasance duk wani abin alherin da ministar ta bijiro da shi sai wasu da dama su maida mata shi sharri, ba tare da bincike ba, saboda kawai an makantar da su daga gani kuma an an toshe masu kunnuwan jin gaskiya.
Ya kamata jama’a su fahimci cewa rumbunan ajiyar kayan abincin Gwamnatin Tarayya, a karkashin Ma’aikatar Harkokin Noma ta Tarayya suke. Saboda haka idan aka bai wa Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa gero ko dawa ko masarar da za a raba, daga can ake sa su a tireloli kai-tsaye a nausa da su jihohin da Gwamnatin Tarayya ta amince a raba kayan tallafin.
Haka nan kudaden tallafin rage radadin talauci da Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ta raba a lokacin korona, wadanda aka ciyar da daliban firamare ‘yan aji 1-3 a lokacin korona, su ma Hukumar Kididdigar Rajistar Marasa Galihu ce ta kididdige su, ita kuma Minista Sadiya ta raba kudade zuwa asusun iyalan marasa galihu domin ciyar da ‘ya’yan nasu. Kuma duk aikin da ministar ke yi, akwai sa-idon Bankin Duniya da kungiyoyin kare hakkin dan’adam da na kare dimokiradiyya masu yawa.
Kafin a maida shirin bayar da tallafi ga Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa bayan an nada Hajiya Sadiya Umar Farouq minista, ana gudanar da shirin ne a karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo. Har aka raba aikin tallafin daga ofishinsa jama’a ba su ma damu da bibiyar yadda ake gudanar da shirye-shiryen inganta rayuwar marasa galihu ba. Sai da aka dawo da shi karkashin ofishin Hajiya Sadiya ne aka yi mata caa, daga mai zagi sai mai aibata ta, kuma duk a ido rufe, babu dalili bayyananne.
Ganin yadda matasa suka rika zakulo kayan tallafin da aka ki rabawa a jihohi ya sa kusan kashi 85 ko ma a ce 90 cikin dari na masu aibata Hajiya Sadiya sun nemi afuwar ta a soshiyal midiya saboda sun gane cewa matar nan da gaskiya take gudanar da ayyukanta. Irin yadda aka rika fiddo kayan tallafin korona a wasu jihohin har wasu sun rube, wasu sun lalace, wasu sun nukake ya sa da yawan mutanen da suka rika yi wa wannan minista makauniyar fassara, sun rika rokon Allah ya yafe masu irin yadda suka rika zagin ta a baya, ba da laifin komai ba. Sun hane cewa wannan matar ta saida ran ta ne da ta rika karakainar raba kayan tallafi a jihohi a lokacin da kowa ya shige gida ya boye, gudun kada korona ta aika da shi lahira. An rika zargin ta a lokacin tana kwange. To yanzu dai gaskiya ta bayyana.
Na ga inda wani malamin jama’a, Halliru Sani, ya bayyana a shafinsa na Facebook fiye da sau goma yana neman afuwar ta. Kuma ya nemi Allah ya yafe masa irin yadda ya rika yi wa Sadiya Allah ya isa a baya, a bisa rashin sani. Shi ma wani mai suna Simon Utsu cewa ya yi: “Duk mai sauran mutunci ya kamata ya roki wannan kyakkaywar mata, Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa afuwar kwandon zagin da suka rika surfa mata.
Ashe mutumiyar kirki ce! Wadanda mu ke kallon na kirkin, ashe su ne baragurbin da suka bar mu a gurbin kuncin rayuwa.
Irin yadda aka rika bankado abincin da aka kimshe aka hana talakawa, bayan Sadiya ta raba ta ba su, ni a nawa kintacen a kowace jiha ba a rasa bankado kayan naira bilyan biyar. Sai nan gaba su rika tara kadamusawa suna raba masu abincin da ba zai ishe su cikin kwana biyu ba. Su kuma mutane su rika rika yi masu kallon mutanen kirki. An dai ji kunya! Ya kamata a tuba da wuri.”
Wani kuma mai suna Sama’ila Lamido ya rubuta cewa: “Ni fa a gaskiya har ba na son shiga Facebook, kada na ga hoton matar nan. Saboda da na ga hoton ta, sai na tuna irin caccakar da na rika yi ina kushe ta. Ashe wadanda suka yaudare mu, suka zalunce mu, suna kusa da mu. Allah mun tuba. Sadiya, ki mana afuwa!” Mustaphan Juwairiya kuma ya ce : “Ina mai neman afuwa da bada hakuri ga Minista Sadiya dangane da aibata ta da na rika yi a bisa zargin kwangen kayan tallafin korona. Ashe ita mai kaunar mu ce. Shugabannin da ke kusa da mu ne ba su kaunar mu.”
Injiniya Adet Ben-Koko ya ce: “Ina ganin lokaci ya yi da za mu ajiye girman kai da ji-da-kai na banza, mu nemi afuwar da yafiyar kyakkyaywar matar nan da muka rika zargin ta boye kayan tallafi ba da wani dalili ba… Mun dai ji kunya kawai!” Shi kuma Franklin Uzoma ga abin da ya ce: “Ina ganin mu daina wani nuku-nuku, mu fito kawai mu nemi afuwar Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa. Allah ka albarkaci wannan mata, amin.”
Uzoma Silas ya ce: “Minista Sadiya ta raba kayan tallafi a Taraba, amma dibgaggun marasa mutunci sun boye. Sai yanzu da Allah ya tona asirin su, gaskiya ta bayyana.”
Wadannan hujjoji da kyawawan shaidu da ke sama sun wadatar, ba sai na kara yin wani bayani ba. Sai dai in kammala da tunatar wa Hajiya Sadiya da sauran jama’a, musamman masu cin moriyar ayyukan ta, cewa da ma Bahaushe ya ce alheri danko ne, ba ya faduwa kasa banza.
Malam Mohammed ya rubuto ne daga Kofar Dan’agundi, Kano