Jami’an tsaro, sun damke mutane 123 da ke da hannu wajen farfasa kayan dakunan ajiyar kayan gwamnati a jihar Filato.
Idan ba a manta ba har zuwa ranar lahadi, ‘yan iskan gari sun far wa dakin ajiyan kayan ayyukan gona na gwamnatin jihar, inda suka fasa dakin da karfin tsiya suka rika kwashe kayan da suke dankare a ciki.
Barayin matasan sun waske da buhunan taki, injinan ban ruwa, magungunan kwari da sauransu.
Dama kuma ranar Asabar ƴan iskan gari sun sun yi gungu sun afka wa dakin ajiyan abinci na tallafin Korona, inda suka farfasa dakin su rika jidar kayan abinci da aka ajiye kafin a fara rabawa mutanen gari.