Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 48 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –18, FCT-13, Kaduna-6, Rivers-5, Ogun-5 da Ondo-1
Yanzu mutum 61,930 suka kamu da cutar a Naj eriya, mutum 57,285 sun warke, 1,129 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,516 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 20,807, FCT –5,961, Oyo – 3,421, Edo –2,648, Delta –1,812, Rivers 2,770, Kano –1,741, Ogun – 1,995, Kaduna –2,611, Katsina -948, Ondo –1,662, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 710, Ebonyi –1,049, Filato -3,587, Enugu – 1,314, Abia – 898, Imo – 614, Jigawa – 325, Kwara – 1,067, Bayelsa – 403, Nasarawa – 478, Osun –922, Sokoto – 162, Niger – 274, Akwa Ibom – 295, Benue – 486, Adamawa – 252, Anambra – 277, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 79, Ekiti – 329, Taraba- 122, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
Yayin da gwamnati ke samun nasaran rage yaduwar cutar korona a kasar Nan gwamnati ta yi kira ga mutanen da kada su karaya wajen kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar.
Gwamnati ta ce ci gaba da kiyaye sharaddun guje wa kamuwa da cutar ce kadai hanyar da wannan ƙasa za ta samu nasaran rabuwa da cutar.
Hanyoyi 10 don gujewa kamuwa da cutar.
1. Yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu.
2. Rufe hanci da baki idan za ayi atishawa.
3. A wanke kuma a dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
4. Rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya.
5. A saka takunkumin fuska musamman idan za a fita ko Kuma Ana cikin mutane.
6. Za a iya amfani da man tsaftace hannu Idan Babu wura da sabulu domin wanke hannu.
7. A rika zama a dakin dake da iska ko Kuma fanka.
8. A rika tsaftace muhalli akai akai.
9. A rage yawan fita Idan ba ya saka dole ba.
10. A rage yawan Zama wurin da akwai chinkoson mutane.
Discussion about this post