Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Rotimi Akeredolu na APC ne ya lashe zaben Ondo.
Ya yi nasara a Kananan Hukumomi 15 daga cikin 18 na jihar.
Eyitayo Jegede na PDP ya zo na biyu, yayin da Agboola na ZLP ne zo na uku.
Jam’iyyu 17 ne su ka shiga takara.
Jegede da ya zo na biyu. A zaben 2016 ma na biyu ya zo, kuma Gwamna Akeredolu din ne ya kayar da shi.
Akwai rikakken bayani ba da dadewa ba.
Sayen kuri’u da bijire wa dokar hana cudanya saboda korona sun rage wa Zaben Ondo armashi -Yiaga Africa
ASHAFA MURNAI
Kungiyar Rajin Kare Dimokradiyya mai suna Yiaga Africa, ta bayyana cewa tsagwaron cinikin saye da sayar da kuri’u da kuma kin bin ka’idar kauce wa kamuwa da cutar korona da aka rika yi, sun rage wa zaben gwamnan jihar Ondo armashi sosai.
Daya daga cikin Shugabannin Yiaga Masu Sa-ido a zaben Ondo, Aisha Abdullahi ce ta bayyana haka, jim kadan bayan kammala zaben a yammacin Asabar.
Da ta ke wa manema labarai bayani, Aisha ta ce, kasuwar sayen kuri’u ta ci sosai a Akoko ta Kudu da Akoko ta Arewa da Akoko ta Kudu.
Sannan kuma ta nuna rashin jin dadin yadda masu jefa kuri’a su ka ki yin amfani da dokar Hukumar Zabe ta Kasa, inda ta umarci masu zabe su rika kaucewa kamuwa da cutar korona saboda gwamutsuwa da jama’a sosai a wurin zabe.
Duk da haka, Yiaga Africa ta jinjina wa INEC saboda kai kayan aiki da wuri, a yankunan da su ka kamata a kai kayan da gaggawa.
Kungiyar ta ce saboda doki da shaukin ganin an kai kayan aiki da wuri ne ya haddasa fitar masu zabe da dama wajen dangwala zabe.
Sai dai kuma Yiaga ta ce a gaban jami’an Yan Sanda a tsaye su na kallon aka rika kokarin nuna wa tsoffin wanda za su akalla.
A zaben dai PREMIUM TIMES ta bi diddigin yadda aka yi zabe, kuma haka ta ma bin diddigin yadda ake tattara sakamakon zabe.
Yiaga Afrika ta nuna farjn ciki da jinjina ga al’ummar Jihar Ondo, saboda an yi zabe kuma ya tafi lani lafiya.
PREMIUM TIMES tuni ta fara bayyana sakamakon zaben wanda ta ce Gwamna Akeredolu ya yi wa sauran yan takara laga-laga a mazabar sa.
Gwamnan Jihar Omdo Rotimi Akeredolu ya samu kuri’a 413 a rumfar zaben za, yayin da sauran jam:iyyu 16 har da PDP su ka tashi da jimillar kuri’u 33.
Rumfar zaben Akeredolu na a karkashin Mazaba ta 6, Rumfa ta 06 a Ijebu Owo, a garin Owon
Sakamakon da aka fitar ya nuna cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 12 kacal, yayin da ZLP ta Mataimakin Gwamna ba ta samu kuri’a ko daya ba.
Sauran jam’iyyu 7 sun samu kuri’a 1 kowace, yayin da jam’iyya daya ta samu kuri’a 9. Wata kuma ta samu 2. Sai wata daya mai kuri’a 3 kacal.
Tun da safe da wakilin PREMIUM TIMES ya isa garin su Akeredolu, wato Owo, babban birnin Karamar Hukumar Owo, ya tabbatar da cewa kaf a garin duk tutocin APC ne, bai ga tutar PDP ko ZLP ko ta wata jam’iyya daya ba.
Da alama sakamakon zaben na nuni da cewa dukkan ‘yan takara manya su uku na APC, PDP da ZLP, kowa ya lashe mazabar sa da tazarar kuri’u masu yawan gaske.
Kowane dan sandan takara dai ya na Shiyyar Sanata daban da sauran.