SOKE RUNDUNAR SARS: Nasara ga Talakawa ko Wasu Tsiraru Marasa Gaskiya, Daga Dallami Hassan

0

Na daɗe ina yin nazarin korafe-korafen da ake tayi game da rundunar tsaro na SARS wanda an kirkiro su ne domin a rage ayyukan ta’addanci, da barayi musamman masu sata da damfara ta yanar gizo wato ‘Yahoo Boys’.

Tun da aka fara wannan zanga-zangar da wanda ya san su da wadanda bai san su ba duk sun bi ayari kowa a soke su, kowa a rusa su.

Kiran da ake yi shine wai jami’an SARS din na muzguna wa mutane, wanda hakan ya saba wa dokar kasa.

Amma ida kuma aka duba ta wani gefen idan Bera na da Sata, daddawa ma na da wari. Mafi yawan mutanen da suka dage sai an soke wannan runduna ta SARS ba mutane bane masu gaskiya. Idan dai ba bisa tsautsayi da ajaliba, sai an zarge ka da wani abu na rashin gaskiya sannan ne za ka ga SARS na neman ka. Haka kawai ba za su rika binka ba don su muzguna maka, sai dai abinda ba a rasa ba. Hatta manya masu kudi kan yi amfani da irin wadannan mutane wajen taya su yin harƙƙallar wasu kuɗaɗen su da suka tara ba da gaskiya ba, amma SARS sun sa su a gaba.

Ko dai kai abokin mai laifine ko kuma mai laifi. Ba zan ce babu wadanda tsautsayi kan fada musu ba amma a gaskiyar magana shine mafiyawan wadanda ke fadawa hannun su duk ba mutane bane masu gaskiya.

Ku duba, irin mawaki kamar Naira Marley, kiri-kiri an tabbatar cewa yana sata da damfara ta yanar gizo, duk da wannan zargi na gaban alkali amma wai shine ke kokarin jan zuga a yi zanga-zangar rusa wannan runduna na SARS.

Toh, haka duk wadanda suke ta korafin a soke su.

Babbar abin da na ga ya fi dacewa shine da an yi wa rundunar garambawul ne maimakon a rusa ta kaf din ta.

Suna ce SARS ne ba aso ko, amma kuma jami’ai, ƴan sanda ne har yanzu kuma ba sallaman su aka yi ba. Saboda haka za su ci gaba da aikin su a matsayin su na Ƴan sanda.

Share.

game da Author