#EndSARS: OPC ta gargadi ‘yan iskan Lagos cewa barnar da su ka yi ta isa haka

0

Kungiyar Kare Kabilar Yarabawa Zalla (OPC), ta gargadi duk wani dan iska da barawon da ke wasoson dukiyar jama’a da sunan zanga-zanga, to su daina hakanan.

Mataimakin Shugaban Kungiyar mai suna Wasiu Afolabi ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya fitar kuma ya sa mata hannu.

Afolabi ya yi bayanin bayan tsshi daga taron shugabannin kungiyar, inda ya kara da cewa “idan ba su daina haka nan ba, to OPC za ta fito da matasan ta domin su tabbatar da tsaro.

Kungiyar ta nuna rashin jin dadin harbin da sojoji su ka yi wa masu zanga-zsnga a Lekki da kuma ysdda tarzoma ta barke har aka rika lalata kayayyakin gwamnati da na jama’a.

Ta roki kuma ta gargadi masu zanga-zanga su daina, saboda sun yi mummunar barna.

Akalla an banka wa ofishin ‘yan sanda 10 wuta a Lagos, baya ga muhimman wuraren da aka sace kayan ciki, aka lalata kuma aka banka wa wuta.

OPC ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da Gamma Babajide Sanwo-Olu su kafa kwamitin bincike na tarayya da na jiha, wanda zai binciki yadda abin ya faru, a kamo masu laifi a hukunta su.

Ya ce bai yiwuwa a bar wadanda su ka bude wa masu zanga-zanga wuta ba tare da an hukunta su ba.

OPC ta nuna takaicin yadda wasu batagari su ka kwace ragamar zanga-zanga daga hannun masu zanga-zangar lumana na #EndSARS.

Share.

game da Author