Gwamnati jihar Kebbi ta bayyana cewa mutum 328 sun kamu da cutar amai da gudawa da ake kira ‘Gastroenteritis’ a jihar.
Hakan ya faru a dalilin ambaliyar ruwan saman da aka yi a jihar inda ambaliyar ruwan ya gurbata ruwan shan da mutanen ke amfani da shi a jihar.
Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Muhammad-Abdullahi Bubuce ya Sanar da haka ranar Asabar yana mai cewa wannan cuta ta bullo a kanana hukumomin hudu a jihar.
Babuce ya ce tuni dai ma’aikatar ta dauki matakan dakile yaduwar cutar.
” Zuwa yanzu mutum 328 ne suka kamu da cutar sai dai kananan hukumomin Kalgo, Sakaba, Maiyama da Suru sun fi fama da barkewar cutar.
” Ma’aikatar lafiya ta jihar ta wadatar da isassun magungunar wannan cuta a asibitoci domin kula da wadanda suka kamu da ita.
Babuce ya yi kira ga mutanen da su tsaftace jiki da muhallinsu domin guje was kamuwa da cutar.
” Sannan a yi kokari a gina bandakuna a gidaje saboda yin bahaya a waje na daga cikin matsalolin dake sa a kamu da cutara.
Wata majiya ta bayyana cewa cutar ta yi ajalin wasu mutane a jihar sai dai Babuce bai tabbatar da adadin yawan mutanen da suka mutu ba.
Sannan wasu da suka warke sun kara kamuwa da cutar saboda rashin samun tsaftattacen ruwa.