Kakakin Yada Labarai Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa babu wani bangaren da ake so Buhari ya yi magana a kai da bai yi magana a kai din ba.
Adesina ya ce duk abin da ake so Buhari ya yi magana, duk ya yi.
Kakakin na Buhari ya yi wannan magana a wata hira da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Channels inda ya ce Buhari ya ce komai, duk kuwa da korafe-korafen da ake yi cewa bai yi magana a kan kisan da ake zargin sojoji sun yi wa masu zanga-zangar #EndSARS ba Lekki.
Adesina ya ce Buhari ya na sane bai yi magana a kan abin da ya faru a Lekki ba, saboda Hedikwatar Tsaron Sojoji da kuma Gwamnatin Jihar Lagos sun kowa ya kafa kwamitin bincike, kuma ba su ma kammala ba, ballantana su mika wa Shugaba Muhammadu Buhari rahoton har ya gani.
Jama’a da dama a cikin gida da kasashen waje sun yi tir da kisan da kuma yadda Buhari ya ki cewa komai a kan abin da ya faru din a Lekki.
Da Adesina ke magana kan taron gaggawa da Buhari ya yi tare da wasu tsoffin shugabannin kasar nan, Adesina cewa ya yi jinjina wa Buhari su ka yi a wurin taron, sannan kuma su ka ba shi shawarwari dangane a halin da kasar ke ciki.
“Wato kasa kamar Najeriya mai mutane kimanin milyan 200, babu yadda za a yi su yi wa wani lamari fahimtar bai-daya. Yadda wannan zai fahimci abu daban da yadda wasu za su fahimta.
” Shugaban Kasa ya tabo babutuwa, ciki har da batun tsaro da tattalin arziki da sauran su.
“A bangaren kasashen waje kuma ya yi bayani, har ya shawarci kasashe su daina gaggawa wajen yanke hukunci tun kafin sahihin bincike ko hujjoji su tabbata.” Inji Adesina.