Kwamitin shugaban don dakile yaduwa da Korona ya fidda sabbin dokoki cutar wanda muta e za su rika bi daga yanzu.
Kodinatan kwamitin Sani Aliyu ya bayyana haka a taron da kwamitin ta yi da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Aliyu ya ce hukumar NCDC da ma’aikatar ilimi suka tsara wadannan sabbin dokoki.
Ya yi Kira ga duk makarantu da su kiyaye wadannan dokoki domin kare yaran makaranta da malamai a daidai wannan lokaci da za su dawo makaranta.
Dokokin
1. Dole Makarantu su samar da kafar sada zumunta da zai hada da iyayen yara, mahukuntar makarantar da jami’an kiwon lafiya na kananan hukumomi.
2. Makaranta za ta samar da kafar sada zumunta domin wayar da malamai, dalibai da iyaye kan matakan gujewa kamuwa da cutar korona.
3. Makarantu su tabbatar duk wanda zai shiga makaranta sai an yi masa gwajin Korona sannan a duba yanayin zafin jikin sa.
4. Dole kowa ya saka takunkumin fuska da kuma man tsaftace hannaye.
5. Makarantun kwana za su samar da wurin yin gwajin cutar sannan da wurin kebe wadanda tsautsayin kanuwa da cutar ya afka musu.
6. Mahukunta za su samar da ruwa da sabulu domin wanke hannu a harabar makaranta.
7. Dole a horas da ma’aikatan lafiya na kowanne makaranta kan yadda za su kula da wadanda suka kamu da cutar tare da Samar wa ma’aikatan kayan kariya.
8. Makaranta za ta nemi izinin iyaye domin kwantar da dalibi koda wani cikin su ya kamu da cutar.
Tuni dai jihohi da dama suka sanar da ranakun bude ta makarantu domin dalibai su koma karatu.