Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta za ta rabawa yara har miliyan 2.1 maganin zazzabin cizon sauro a jihar Barno.
Jami’in Hana yaduwar cutar na WHO Iniabasi Nglass ya sanar da haka a sansanin ‘yan gudun hijira dake Elmiskin.
Ngalss ya ce kungiyar za ta Bai wa Yara masu shekaru 3 zuwa watanin 59 maganin cutar a kananan hukumomi 25 a jihar.
Ya ce a shekarar 2019 kungiyar ta raba wa yara magunguna a kananan hukumomi 25 dake jihar ta hanyar hadinguiwa da ta yi da malaman addinai da sarakuna.
Bayan haka kodinatan dakile yaduwar zazzabin cizon sauro na WHO Mala Waziri ya ce a bana WHO za ta bai wa yara maganin zazzabin cizon sauro 20,000 a sansanin domin Kare su daga kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba a watan Janairu gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta ciwo bashin dala miliyan 890 daga asusun duniya domin dakile yaduwar cututtuka a kasar nan.
Gwamnati ta ce za ta kashe wadannan kudade wajen yaki da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro da tarin fuka daga shekarar 2021 zuwa 2023.
Shugaban kwamitin sa ido kan tallafin da asusun duniya ke bai wa Najeriya (CCM) Dozie Ezechukwu ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Ezechukwu ya ce bisa ga kason kudaden da gwamnati ta yi zazzabin cizon sauro zai dauki babban kaso daga cikin wadannan kudade da ya kai dala miliyan 417, kanjmau, dala miliyan 329 sannan tarin fuka dala miliyan 143.
Ya kara da cewa gwamnati ta tsara matakan da za su taimaka mata wajen kashe wadannan kudade yadda ya kamata ba tare da wani ko wasu sun yi sama da fadi da su ba.