Ba yau ba, ba jiya ba, a lokuta daban-daban, mutane daban-daban, manya da matasa, masu ilimi da akasinsu sun sha kai-komo da cece-kuce dangane da sake fasalin Najeriya a hukumance da kuma ta fannin gudanarwa. Wasu ma sun nemi a raba kasar, kowa ya kama gabansa. Irin wadannan takaddomi ne suka sanya masani kuma marubuci, Dokta Bukar Usman, OON ya rubuta littafi mai suna Restructuring Nigeria: An Overvew, Ma’ana: Sake Fasalin Najeriya:
Abubuwan La’akari. Ganin irin muhimmancin sakonnin da ke kunshe a littafin ya sanya GIZAGO ya bijiro da tsakure da sharhi a wannan shafi:
Shin wai yanzu sai a wayi gari a ce maka za a sake fasalin zamantakewar Najeriya, to ta ina za a fara, me da me za a yi la’akari da su kafin a cin ma sake fasalin kasar? Shin yawan al’ummar yanki ko gari ko yawan fadin kasa ko al’ada ko addini za a lura kafin a ce an sake fasalin kaza da kaza na Najeriya? Wadannan da ma wasu muhimman abubuwan lura kuma masu matukar muhimmanci, su ne kunshiyar wannan mashahurin littafi na Dokta Bukar Usman.
Wannan littafi, tun da farko marubucinsa ya sadaukar da shi ne kacokan ga “Hadin Kan Jamhiriyyar Najeriya, Shugabancin Adalci, Tsaro da Zaman Lafiya da Walwalar Al’ummar Najeriya.”
Kamfanin da ya wallafa littafin ma ba a bar shi baya ba, domin kuwa ya bijiro da wani tsokaci da ke tambihi game da muhimmanci ko rashinsa na tukaddima game da al’amuran kasa. Ya buga misali da wasu tukaddimomin jin ra’ayi da aka sha fafatawa a zamanin gwamnatoci daban-daban da suka shude, inda daga karshe kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Ya doka misali da wata takaddama da aka taba yi game da alfanu ko rashin alfanun ciwo bashi daga Asusun Babban Bankin Duniya (IMF), a shekarar 1985, inda daga karshe dai mafi yawan masana da al’ummar kasa suka nuna adawa da ciyo bashin amma daga bisani sai gwamnatin lokacin ta yi gaban kanta.
Ba ta ciyo bashin ba amma ta kawo tsare-tsaren da bankin ya kakaba mata, matakin da ya kasance wa kasar gaba kura baya sayaki. A lokacin nan aka karya darajar Naira, aka kawo tsarin Kowa Ya Ji A Jikinsa (SAP). Tun daga lokacin kuwa darajar Naira ta yi ta zagwanyewa har
zuwa wannan zamanin, idan aka kwatanta ta da Dalar Amurka.
Baya ga wannan, a shekarar 1994/1995, gwamnatin lokacin ta gabatar da Kwamitin Sake Fasalin Tsarin Mulkin Kasa, inda membobi suka shawarta samar da tsarin shugabancin kasa na karba- karba a shiyyoyi shida na Najeriya. Sun bukaci kowane Shugaban Kasa ya yi mulki na shekara shida sau daya, sannan ya ba wani shi ma daga wannan yanki zuwa wancan yanki. Sai dai kuma abin mamaki, lokacin da aka zo samar da Kundin Tsarin Mulki a shekarar 1999, sai aka yi watsi da wannan batu na karba-karba.
Ga shi dai Najeriya na da Kundin Tsarin Mulki, ga shi ana mulkin dimokuradiyya, ga Majalisun Tarayya da na Jihohi da na Kananan Hukumomi amma har yanzu ana tada jijiyar wuya, cewa a sake fasalin kasa – to ta yaya za a cin ma wannan kuduri kuma me ya sa har kullum ake tado da batun?
Kamar yadda aka gabatar a littafin nan, akwai bukatar a yi la’akari da abubuwa muhimmai gudabakwai, a duk lokacin da aka taso da maganar sake fasalin kasar nan:
1 – Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya samar da tanajin da ake bukata, a duk lokacin da ake son canja wani tsari ko fasali da ya shafi kasa da al’ummarta.
2 – Da gangan aka samar da tanaje-tanaje masu rassa daban-daban domin ya gajiyar da duk wani mai son kawo rabuwar kan al’ummar kasa. Ta haka ne hadin kan al’umma zai wanzu, kasancewar kowa na bukatar kowa.
3 – Ba daidai ba ne a ce za a yi watsi da Kundin Tsarin Mulki na 1999, domin kuwa duk da cewa a karkashin Gwamnatin Soja aka samar da shi, amma dai farar hula sun shiga ciki dumu-dumu, tare da su aka dama kuma da su aka sha kuma ake kan sha har yanzu.
4 – A can baya, an yi watsi da Tsarin Mulkin Falamantare ne saboda ra’ayin al’umma da suka ce tsarin yana ba yankuna karfi fiye da kima, wanda haka ya sanya babu hadin kan kasa, don haka dole aka yi watsi da shi; inda jihohi suka raba dukkan dukiya kasa daidai-wa-daida, ba su rage komai ba.
5 – Masu da’awar cewa ya kamata a koma tsarin mulkin 1963 na Falamantare lallai hakan na da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa, musamman idan aka yi la’akari da cewa a yanzu an samu karuwar al’umma, an samu sabbin hanyoyin kudin shiga da tattalin arzikin kasa da sauransu. To, ta ina za a soma komawa baya kuma a ce za a samu fa’ida?
6 – Idan aka natsu aka lura, za a fahimta da cewa matsalolin da ke tattare da gudanar da gwamnati suna da matukar yawa, don haka wani sake fasalin kasa a siyasance ba shi ne zai magance matsalolin ba.
7 – Babu wani abu da zai kawo wa kasar nan fa’ida da aminci da zaman lafiya da ci gaba, face CANJIN HALAYYA daga shugabanni da ’yan kasa baki daya zuwa na gaskiya da adalci da kyautata yi da kishin kasa da na al’umma.
Masu hankoron sake fasalin Najeriya dai daga dukkan alamu bulayi kawai suke yi, wai bara a kufai. Duk wani fasali ko wani canji da ake bukata don tafiyar da kasar nan, kamata ya yi a maida shi ga abin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanada. Sai dai abin lura shi ne, babu wani Kundin Tsarin Mulki da ya kasance “kambamau,” marar matsala a duk duniya.
Don haka ne ma ake samun canje-canje daga lokaci zuwa lokaci. Hatta kasar China, duk da tsarin mulkinta ya bambanta da na Najeriya, a shekarar 2018 ta samar da canje-canje a tsarin mulkinta a wurare 21.
Ke nan, tun da dai Najeriya na bin turbar mulkin dimokuradiyya ce kuma akwai Majalisun Kasa tun daga Tarayya zuwa Jihohi da Kananan hukumomi, to kuwa membonbin majalisun nan, hakkinsu ne a matsayinsu na wakilan al’ummun da suka fito, su gabatar da kudurin abin da suke
son a canja, a tattauna a majalisu, a bi dokar tsarin mulki domin canja shi.
Har kullum abin la’akari shi ne, me al’umma ke bukata, mene ne fa’idarsa, ta yaya za a samar da biyan bukata? Sai a shiga Kundin Tsarin Mulki, a ga abin da ya tanatar, idan ana bukatar
kwaskwarima, a bi doka a tabbatar da ita domin fa’idar kasa da al’umma. Hakan shi ne alheri, ba a ce za a samar da wani kwamiti na mutane daban, a kashe kudi, a bata lokaci ba, alhali akwai majalisu da aka tanadar domin wannan aiki.
Wannan shi ne abin yi mai fa’ida, domin kuwa akwai misalin dacewar haka. A 2016 zuwa 2017 ai Majalisun Kasa sun samar da canje-canje a sassa 32 na Kundin Tsarin Mulki.
Alhali tarukan sake fasalin tsarin mulki da gwamnatocin Obasanjo da ta Jonathan suka shirya ba su haifar da wani canji na alheri da ke amfani ba, duk da makudan kudi da lokaci da aka bata.
Babu wani alfanu da kasa ke samu daga kiraye-kirayen sake fasalin kasa sai haddasa rarrabuwar kai, tayar da yekuwar bambancin addini, kabilanci da bangaranci. Wannan kuwa shi ke haifar da zaman dar-dar, tashin-tashina da kallon raini tsakanin al’ummar kasa. Kuma ba wasu ne ke haddasa haka ba, illa wasu ’yan siyasa da ke fakewa da guzuma domin su harbi karsana – domin cikar burinsu amma ba domin ci gaban al’umma ba.
Ke nan, Majalusun Kasa su ne wakilan al’ummar kasa, duk wata takaddama, duk wani canjin fasalin tsarin mulki, su ya kamata su tattauna shi, su samar da hanya sahihiya ta mafita, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanatar. Majalisun za su iya kuma aikinsu ne!
Za mu ci gaba
________
Wannan tsakure da sharhi da Bashir Yahuza Malumfashi ya yi akan littafin Dokta Bukar Usman mai taken “Restructuring Nigeria: An Overview,” ma’ana “Sake Fasalin Nijeriya: Abubuwan La’akari” shi ne kashi na daya wanda an buga a jeridar Aminiya na ranar 14 zuwa 20 ga watan Agusta, 2020 a shafi na 14.