Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta janye jami’an tsaron Magu, “Magu na cikin hadari” – Inji Iyalan sa

0

Majiya mai tushe ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa rundunar ‘yan sandan kasa ta janye duka jami’an tsaron Ibrahim Magu, wadanda ke tare da shi da wadanda suke kula da gidajen sa.

Wani dan uwansa da ba ya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya shaida cewa, yanzu fa Magu na ga hannun Allah ne domin duk an janye masu tare shi gida da waje.

” Ko a dalilin irin aikin da yayi da dubban abokan gaba da yayi a dalilin aikin, bai kamata ace an janye masu samar masa da tsaro ba.

Har yanzu Magu na tsare a hukumar ‘yan sanda, kwanaki hudu bayan an tsare shi domin gurfana a gaban kwamitin binciken bacewar wasu biliyoyin naira da aka kwato a hannun barayin gwamnati.

Da misalin karfe 7:30 na yammacin Talata, Jam’ian tsaro suka dira gidan shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu, inda suka gudanar da bincike.

Daya daga cikin masu gadin gidan ya tabbatar wa Premium Times cewa jami’an tsaron sun dira gidan Magu dake Maitama da kuma gidan sa na kan sa dake Karu.

Ya kara da cewa bayan sun gama binciken gidan, sako sako, daki dai, kurdi-kurdi sai suka fito suka ba da takar da muka sa hannu.

” Ba su tafi da komai ba.”

Karanta labarin mu na baya

Fadar shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta dakatar da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu. Wannan sanarwa bai bayyana ga manema labarai ba sai dai majiya daga fadar shugaban kasa da hukumar EFCC sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an dakatar da Magu daga cigaba da shugabantar hukumar EFCC.

Idan ba a manta ba Magu ya kwana tsare a hannun jami’an tsaro masu binciken musamman.

Majiya ta tababtar wa PREMIUM TIMES cewa bayan an shafe tsawon lokaci ana yi masa tambayoyi, an bada umarnin a tsare shi a hannun Ofishin ‘Yan Sandan CID da ke Area 10, kusa Hedikwatar Sojojin Sama, na Kasa da na Ruwa.

Majiya daga iyalin sa sun tababtar da cewa bai kwana a gida ba. Haka ma majiya a cikin EFCC ta ce bayan an yi masa tambayoyi daga bakin Kwamitin Bincike, sun bada shawarar a tsare shi a hannun ‘yan sanda.

Magu, wanda ke da mukamin Kwamishinan ‘Yan Sanda, majiya ta ce yayin da wasu ke ba da shawarar a tura shi kotu, wasu kuma a cikin ‘yan kwamitin na ganin cewa a nemar masa mafita mai sauki, wato a sauke shi salum-alum.

PREMIUM TIMES ta bayyana yadda aka tafi da Magu, inda ta ce Jami’an sun yi cacukui da Magu, Shugaban EFCC

Jami’an tsaro sun yi wa Karamin Ofishin EFCC da ke Wuse II kawanya, su ka damke Shugaban EFCC din na Riko, Ibrahim Magu.

An yi awon gaba da shi da rana, bayan jami’an tsaron sun kwashe minti 30 su na tankiya da jami’an tsaron Magu.

Sun dai hana masu tsaron Magu bin su, domin su ga inda aka nufa da shi.

An garzaya da shi cikin Fadar Shugaban Kasa, domin amsa tambayoyi daga kwamitin binciken da Shugaban Kasa ya kafa, domin binciken zargin da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi masa.

Malami dai ya zargi Magu da yi wa shirin yaki da rashawa kafar-ungulu da kuma yi wa wasu kudaden da Hukumar EFCC ta kwato, irin abin nan da Hausawa ke kira ‘sata-ta-saci,-sata.’

Majiya daga EFCC ta ce tuni har lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya garzaya Fadar Shugaban Kasa inda Magu ya ke a yanzu.

Ko EFCC ko SSS babu wanda ya ce komai dangane da kamun da aka yi wa Magu.

Jami’an Yada Labaran su ma da aka kira, kin cewa komai suka yi.

Dalilin Kama Magu: Tuggun Ministan Shari’a Malami Ne – Mamba na PACAC

Daya daga cikin ‘yan Kwamitin Bunkasa Tattalin Arziki na Shugaban Kasa, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa abin da ya samu Magu, kutunguilar neman kara samun shiga ce a wurin Shugaba Muhamadu Buhari, wacce Ministan Shari’a Abubakar Malami ya shirya masa.

Ya ce tun farko Malami bai so aka bai wa Magu rikon EFCC ba, kuma Malami ne ya hada baki da SSS suka rubuta rahoton da ya nuna bai dace Buhari ya nada Magu cikakken Shugaban EFCC ba.

Wannan rahoton ne Majalisar Dattawa ta kafa hujjar kin amincewa d Magu, shi ya sa tun daga 2015 har yau ya ke yin shugabancin riko.

Shi kan sa kamun da aka yi wa Magu, ya bijiro ne bayan Minista Malami ya rubuta taardar zargi a kan Magu.

Ya zargi Magu da karkatar da wasu makudan kudaden da aka karbo. Yayin da shi kuma Malami ake zargin sa da yin amfani da wasu jami’an cikin EFCC ana kai wa Magu hare-haren rubuce-,rubuce a kafafen yada labarai.

Share.

game da Author