Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) dake da ofishi a nahiyar Afrika ta yi Kira ga kasashen Afrika da su gaggauta tsara hanyoyin samar da isassun magungunan kawar da cutar coronavirus a kasashen su yayin da masana kimiya ke kokarin gano maganin da ya fi dacewa ayi amfani don warkar da mutane.
WHO ta ce a yanzu haka akwai magungunan kawar da cutar 150 da aka sarrafa a duniya sannan 19 daga cikinsu yanzu haka tantance ingancin su.
Shugaban hukumar WHO dake yankin Afrika Matshidiso Moeti ya ce yin wannan kira na da mahimmancin gaske saboda a kullum kasashen Afrika sune a baya wajen cigaba musamman a bangarorin kimiya da fasaha, kiwon lafiya da sauran su.
Shugaban majalisar dinkin duniyar UN António Guterres a nashi tsokacin ya ce kamata ya yi idan an gama hada maganin lallai a tabbatar kowace kasa ta samu, akad a kebe wasu a bar wasu.
Ya ce kasashe masu tasowa na cikin kasashen kasashen duniyan da ya kamata a tabbatar sun samu isassun maganin cutar.
Discussion about this post