Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 16 a kauyen Kukum Daji.
Wani mazaunin Sabon Garin Manchok ya bayyana cewa mahara sun afka wa gungun masu bukin aure Inda suka dira suna harbi ko ta ko Ina.
A sanadiyyar haka mutane da yawa sun tsira da muggan raunuka a jikinsu baya ga wadanda maharan suka kashe.
Kwamishinan tsaron jihar da Harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya shaida wa manema BBC Hausa cewa gwanati na ganawa da mahukuntan Karamar Hukumar Kaura da masu fada aji na yanki domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda.
Jihar Kaduna Kamar jihar Zamfara da Katsina na fama da hare-haren ‘Yan ta’adda da ‘yan bindiga.
Idan ba a manta ba a Cikin makon jiya mahara suka kashe Sojoji 16 a karamar Hukumar Jibia dake jihar Katsina.