Da safiyar Litinin ne aka sanar da rasuwar Alhaji Inuwa Abdulkadir.
Sanata Shehu Sani, ya bayyana rasuwar Inuwa a shafin sa ta tiwita.
Inuwa ya rasu bayan yayi fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya ranar litini.
Kafin rasuwar sa, marigayi Inuwa shine tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa Maso Yamma.
Waziri Bulama, shima ya bayyana cewa ko da ya hadu da marigayin bai ga alamun rashin lafiya tare da shi.
Ya tabbatar da rasuwar sa.
Za a yi jana’izar marigayi Inuwa ranar litinin da misalin karfe biyu a gidan sa dake Sokoto.