Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 544 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 99, Ebonyi 65, Oyo 47, Ondo 46, Ogun 31, Edo 30, FCT 28, Katsina 25, Filato 15, Bayelsa 11, Kaduna 10, Adamawa 10, Akwa Ibom 8, Gombe 7, Kano 4, Taraba 3, Rivers 2, Abia 2, Ekiti 1.
Yanzu mutum 28711 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 11665 sun warke, 645 sun rasu. Zuwa yanzu mutum 16, 401 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 11, 244 cases, followed by FCT – 2,181, Oyo – 1,513, Edo – 1,383, Kano – 1,268, Delta – 1,227, Rivers – 1,183, Ogun – 1,005, Kaduna – 865, Katsina 604, Borno – 528, Bauchi – 516, Gombe – 520, Ebonyi – 456, Filato – 436, Ondo – 456, Abia – 385, Enugu – 372, Imo – 352, Jigawa – 318, Kwara – 269, Bayelsa – 245, Nasarawa – 225, Osun – 165, Sokoto – 153, Niger – 122, Akwa Ibom – 112, Benue – 97, Adamawa – 99, Kebbi – 84, Zamfara – 76, Anambra – 73, Yobe – 61, Ekiti – 44, Taraba – 22, da Kogi – 5.
Idan ba a manta ba, a ranar Talata, kungiyar kiwon Lafiya ta duniya (WHO), ta bayyana cewa yanzu ne duniya za ta afka cikin babban bala’in Coronavirus.
Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya fitar ya ce a baya ba a ga komai ba tukunna.
Tedros wanda aka buga bayanin sa a BBC da rumbun tattara bayanan kamuwa da kisan adadin mutane sakamakon Coronavirus, wato worldometers.org suka wallafa, ya ce matsawar gwamnatocin kasashen duniya ba su gaggauta tashi tsaye sun yi da gaske ba, to wannan cuta za ta yi wa duniya rundugun da ya wuce wanda ake ciki a yanzu fiye da kima.