Yadda mahara suka sace mahaifin tsohon gwamnan Filato, Pa Defwan Dariye

0

Masu garkuwa sun sace mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, Pa Defwan Dariye.

Kakakin rundunar ‘Yan sanda jihar Filato Ubah Ogaba ya shaida wa manema labarai cewa mahara sun yi awon gaba da dattijo Pa Defwan Dariye da sanyi safiyar Alhamis.

An sace Pa Dariye a gidansa dake Mushere, Karamar Hukumar Bokkos.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta taba ruwaito yadda aka sace mahaifin Dariya a shekarar 2015.

Kakaki Ogaba ya ce tuni jami’an ‘yan sanda da mutan gari sun fantsama neman inda aka arce da dattijo Dariye.

Dan sa kuma tsohon gwamnan jihar Filato, Josua Dariye ya daure a gidan kaso bayan samun sa da aka yi ya wafce da kudaden jihar a lokacin da yake gwamnan jihar Filato.

Share.

game da Author