Daya daga cikin dan hadimin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua a lokacin da yake gwamnan jihar Katsina, ya bayyana cewa mahaifinsa yayi fama da gajeruwar rashin lafiya kafin Allah yayi masa rasuwa.
Marigayi Rabiu Musa ya rasu a asibiti a birnin Kano bayan fama da yayi da gajeruwar rashin lafiya.
Dan sa, Musa rabiu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mahaifinsa mai shekaru 60 a duniya ya fara jin zazzabi da makaki a makogoron sa. bayan dan wani lokaci sai ya samu sauki. Haka kuma ba a dade ba sai ya ce yana jin numfashin shi na yankewa akai-akai, daga baya sai yace daukewa take yi kwata-kwata musamman idan ya gashi.
Da misalin karfe 3 na dare Allah yayi masa cikawa a asibiti a Kano.
Musa ya ce ba a kai ga karbar sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa mahaifinsa ba ya rasu.
Allah yaji kansa.