Amurka ta maido wa Najeriya Dala Miliya 311, kudin da Abacha ya wawushe ya kimshe a waje

0

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da maido da dala miliyan 311 da kasar Amurka tayi wa Najeriya cikin kudaden da tsohon shugaban Kasa marigayi Sani Abacha ya kimshe a kasar.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa tuni har gwamnatin Najeriya ta kimshe kudaden a asusun babban bankin Najeriya, inda daga nan za a yi amfani da su wajen aikin gina hanyoyin, Legas-Ibadan, Abuja-Kano da gadan Neja dake yankin Kudu maso Gabas.

Malami ya ce kudin ya karu ne saboda ajiya da ya sha a asusun banki a kasar Amurka da New Jersey.

Yace Najeriya ta samu karin dala miliyan uku kudin ruwa daga ajiyar tun bayan fara tattauna maido da kudin da akayi da tawagar Najeriya da gwamnatin Amurka.

Idan ba a manta ba, gwamnatin Buhari ta amso wasu kudade irin haka da suka kai dala miliyan 322 daga kasar Switzerland.

Cikin 2017 ne Gwamnatin Switzerland ta maido wa Najeriya dala milyan 332.5, kwatankwacin naira bilyan 125, daga cikin makudan kudaden da Sani Abacha ya sace daga Najeriya ya boye a can kasar.

Sai dai kuma an kafa yarjejeniya cewa Bankin Duniya (World Bank) tare da wasu kungiyoyi za su sa ido a kan yadda talakawa za su amfana da kudin, don gudun kada wasu batagarin jami’an gwamnati su sake sace kudaden.

Wannan kudi ya zo a wa Najeriya a kan gaba, a wannan lokaci da ake fama da karancin kudade a duniya a sanadiyyar annobar coronavirus da ya karade kasashen duniya.

Saidai kuma kamar yadda minista Malami ya ce, wannan kudi za a kashe su a ayuukan gina tituna da gadar Neja.

Share.

game da Author