Kungiyar Likitoci (ARD) reshen jihar Ogun ta Sanar cewa mambobin kungiyar sun fara yajin aiki na kwana uku domin jawo hankalin gwamnatin jihar game da alkawurran da ta dauka bata cika ba.
Shugaban kungiyar Mutiu Popoola da sakataren Kungiyar Tope Osundara ne suka sanar da haka a wani takarda da suka sakawa hannu ranar Lahadi.
Bisa ga takardar, ARD ta ce za ta fara Wannan yajin aiki ne daga ranar saboda rashin cewa komai da gwamnati ta yi game da alkawurran da ta dauka a kan su.
Alkawuran da gwamnati ta dauka kuma ta kasa cikawa sun hada da rashin biyan su alawus, rashin samar wa ma’aikatan kiwon lafiya inshorar lafiya, da kin fara biyan su da sabon tsarin biyan albashi da sauran su.
“Muna bukatan gwamnati ta biya duk ma’aikatan kiwon lafiya a jihar alawus din su da ke makale a wurin ta musamman na aikin kula da wadanda suka kamu da cutar Covid-19.
“A watan Afrilu gwamnati ta kara yawan alawus din ma’aikatan mu daga naira 5000 zuwa 15,000 sai dai gwamnati ta biya wadannan kudade sau daya kacal.
Sai dai ta ce wannan yajin aiki bai hada da likitocin dake duba masu fama da cutar COVID-19 ba.
Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar Hana walwala a jihohin Legas da Ogun da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Daga ranar 4 ga watan Mayu, za a ci gaba da walwala tun daga karfe 9 na safe zuwa karfe 8 na dare, daga nan kuma za a shiga kulle sai safiyar gobe.